Zan yi Nazari Sakin Nnamdi Kanu – Buhari

Date:

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai yi nazarin buƙatar da ya kira “mai girman gaske” ta neman ya saki Nnamdi Kanu wadda ƙungiyar dattawan al’ummar Ibo suka gabatar masa.

Mista Kanu wanda ake zargi da aikata ta’addanci a gaban kotu, na hannun ‘yan sandan farin kaya na DSS sakamakon gwagwarmayar da yake yi ta neman kafa ƙasar Biafra a kudancin Najeriya ƙarƙashin ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da aka haramta.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin dattawan a fadarsa da ke Abuja ranar Juma’a ƙarƙashin jagorancin tsohon Ministan Sufurin Jirgin Sama Mbazulike Amaechi.

“Kun nemi abu mai matuƙar girma a wajena a matsayina na shugaban wannan ƙasa. Tasirin buƙatar taku na da girma sosai,” a cewar Buhari cikin wata sanarwa da Femi Adesina ya fitar.

Ya ƙara da cewa buƙatar da dattijan suka nema “ta saɓa wa tanadin tsarin mulki da ya fayyace tsarin shugabanci tsakanin gwamnati da ɓangaren shari’a”.

“Sai dai buƙatar da kuka gabatar mai girma ce sosai amma zan yi nazari a kanta,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...