Haɗewar Kwankwaso da Shekarau ba abin tsoro ba ne ga APC – A A Zaura

Date:

 

Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iya mai mulki ta APC, Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya ce ko da tsohon gwamnan Jihar, Rabi’u Kwankwaso da Sanata Ibrahim Shekarau sun haɗe kansu, hakan bai zai razana jam’iyar ba.

A wani fefen bidiyo da ya yi hira gidan talabijin na TrustTV, Zaura, wanda a ka fi saninsa da A. A. Zaura, ya baiyana cewa ra’ayin Kwankwaso da Shekarau ne su ga cewa ya dace su haɗe da junansu a siyasa.

A cewarsa, ko da sun haɗe ɗin to hakan ba zai zama barazana ga APC ba domin jam’iyar ta na da ƙarfi a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Zaura ya ƙara da cewa ita nasara daga Allah ta ke kuma ko mutu ya na ganin cewa idan ya fita da ga jam’iya za a samu rashin nasara, sai kuma akasin haka ya faru.

“It dai nasara da ga Allah ta ke. Ko mutum ya na ganin cewa ya na da ƙarfin da idan ya fita da ga jam’iya za ta samu matsala, to yawanci sai ka ga ba haka bane. Sai ka ga hakan ya zamo nasara ma ga jami’yar.

“Kawai dai ana bukatar haɗin kai da haɗa ƙarfi da karfe domin a cimma nasara,” in ji Zaura.

Da a ka yi masa tambaya a kan ko da yiwuwar sulhu tsakanin Shekarau da Gwamna Abdullahi Ganduje, sai Zaura ya ce ba zai iya cewa komai ba saboda abokan juna ne kuma sun yi aiki tare, inda ya ƙara da cewa ba abin mamaki ba ne wataran a ga sun shirya.

Daily Nigeria ta rawaito Ya kuma ƙara da cewa shi ba shi da wata matsala da Shekarau saboda ya ɗauke shi uba, haka shi ma Ganduje uba ne gare shi kuma jagora, in da ya ƙara da cewa babu komai tsakaninsa da shugabannin biyu sai girmamawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ga Duniya baki daya – Shugaban kamfanin Yahuza Suya

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Shugaban kamfanin Yahuza Suya & Catering...