Wasu Jami’an lafiya daga Sokkoto sun ziyarci Kano don Koyan aikin kula fa lafiya

Date:

Daga Kabiru Harun Yakasai

 

Darakta Janar na Hukumar Samar da Magunguna ta Jihar Kano, Pharmacist Hisham Imamuddeen ya karbi bakuncin rukunin wasu jami’ai daga ma’aikatar lafiya ta Jihar Sakkwato a rangadin binciken da suka kai hukumar a ranar Larabar data gabata.

Tawagar da ta kai ziyarar, ta kunshi manyan jami’an gudanarwa na ma’aikatar wanda ke karkashin jagorancin Pharmacist Murtala, da sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin kula da lafiyar al’ummar jihar Sokoto.

Cikin wata sanarwa da jami’ar yada labarai ta ma’aikatar lafiya ta jihar kano Hadiza M Namadi ta aikowa kadaura24 tace Pharm. Hisham Imamudeen, a yayin da yake yi musu bayani kan ayyuka da kuma nasarorin da hukumar ta samu a baya-bayan nan, ya kuma yabawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa yadda yake bayar da goyon baya ga fannin lafiya.

Ya bayyana matukar jin dadinsa da godiya ga Gwamna bisa yadda ya ware kaso mai tsoka ga fannin lafiya a cikin daftarin kasafin kudin shekarar 2022 da kuma tallafawa hanyoyin samar da kayayyaki duk da nufin inganta rayuwar al’ummar jihar kano.

Tun da farko a jawabin nasa, Shugaban Kungiyar, Pharm. Murtala ya ce sun zo Kano ne domin ganin irin aiyukan da hukumar take saboda su ma su yi koyi don su inganta hukumarsu tare da bunkasa lafiyar al’umma.

Daga nan Pharm. Murtala ya bayyana jin dadinsa da abin da suka gani, don haka ya yaba da aiyukan da aka suka gani da irin tarbar da aka yi musu,sannan ya yi alkawarin yin koyi da tsarin jihar Kano wajen inganta harkar samar da kayayyakin kula da lafiya a jiharsu.

Ya kuma godewa DG da daukacin ma’aikatan gudanarwar sa bisa karramawar da suka yi masu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...