Babban taron yan Majalisun Africa zai kawo sauyi a wakilcin al’umma – Dogowa

Date:

Daga Mardiyya Ahmad Daneji
Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta kasar nan kuma dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Tudun wada da Doguwa Hon. Alhassan Ado Doguwa ya bayyana cewa babban taron yan majalisun  kasashen Africa zai haifar da kyakykyawan sakamako ga al’ummar Africa baki daya.
Shugaban masu rinjayen ya bayyana hakan ne yayin babban taron yan majalisun kasashen Africa wadanda suke rainon ingila, wanda Nigeria take daukar nauyinsa yanzu haka a babban birnin tarayya Abuja.
Alhassan ado wanda shi ne Sardaunan Rano yace dama akan shirya taron a lokuta daban-daban ,inda ake tatattaunawa kan muhimman batutun da zasu tallafawa rayuwar al’ummar Africa baki daya.
Yace taron wanda shi ne karo na 51 zai mai da hankali ne wajen inganta wakilcin da yan majalisu suke yiwa al’ummar da kuma samar da hadin kan yan majalisun kasashen Africa da kuma tabbatar da yin dokoki wadanda zasu inganta rayuwar al’ummar da suke yiwa wakilci.
” Majalisar kasar nan ce ta dauki nauyin taron kuma dama haka ake, kamar yadda akai a kasashen Ghana Camaroon da dai sauran Manyan  kasashen Africa, an tattauna matsalolin da suke addabar kasashen Africa musamman ta’addaci, shaye-shayen miyagun kwayoyi, da matsalolin da Demokaradiyya take fuskanta musamman batun juyin mulki da ake samu a wasu kasashen Africa a baya-bayan nan” . inji Doguwa
Alhassan Doguwa ya yi fatan a karshen taron dukkanin yan majalisun da suka halacci taro zasu kara samun gogewa ta yadda zasu ingata aikinsu don amfanin al’ummarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...