Yanzu-Yanzu: Ganduje ya yiwa Majalisar Zartarwa ta jihar kano Garanbawul

Date:

Daga khadija Abdullahi

Gwaman jihar kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje bayan ya rantsar da sabon kwamishina Engr. Idris wada Sale wanda majalisar dokokin jihar kano ta amince da nada shi a matsayin kwamiahina, ya gudanar da sauye-sauye a cikin majalisar zartarwar jihar kano.
Kadaura24 ta rawaito Ganduje ya jagoranci rantsar da sabon kwamishinan ne a yayin taron majalisar zartarwar jihar kano na wannan makon wanda ake gudanarwa a gidan gwamnatin kano.
Gwamnan yace sabon kwamishinan an tura shi ma’aikatar aiyuka ta jiha ,yayin da kwamishinan dake Ma’aikatar wato Idris Garba Unguwar Rimi aka mayar da shi ma’aikatar kimiyya fasaha da ƙirƙira ta jihar kano.
Sabon kwamishinan dai kafin wannan lokaci shi ne manajan daraktan hukumar karma ta jihar kano .
Tuni dai kwamishinan ya fara aiki domin ya zauna zaman majalisar zartarwar jiha na wannan makon.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...