Kwamittin mauludin Gidan marigayi Alh uba waru ya gudanarda mauludin fiyayyen halitta annabi sallallahu Alaihi wasallam kamar yadda mihaifinsu yake gudanarwa a lokacin yana Raye.
Alhaji faruk uba waru ya bukaci iyaye dasu Kara Sanya soyayyar Annabi sallallahu Alaihi wasallam a zukatan ƴaƴansu Wanda yin hakan zai tallafa wajan samun Al’umma ta gari.
Yace iyaye basu da abun da zasu yiwa ƴaƴansu fiye da basu ilimin addini wanda zai sa su san martaba da darajar Annabi (S A W) da kuma koyi da halaye da ɗabi’unsa.
Shi ma a nasa jawabin Alkali Halhalatul kuza’i Zakariyya ya bayyana cewa al’ummma jihar kano mutane ne masoya annabi S A W da kuma sahabbansa, inda yace hakance tasa suke gudanar da bikin tunawa da ranar haihuwa fiyayyan halitta annabi Muhammad sallallahu Alaihi wasalam .
Ya buƙaci al’ummar jihar kano su mai da hankali wajen yin addu’ar samawa kano da Nigeria zaman lafiya da cigaban tattalin arziki.
Taron mauludin ya samu halarta malamai da sha’airai daga fadin jihar nan wadanda suka hadarda sakataren majalisar shura na Tijjaniyya sheikh Barrister Habib Muhammad Dan Almajiri da dai sauransu.