Buhari ya tafi Scotland Kwana biyu bayan ya dawo daga Saudia

Date:

Kwana biyu bayan dawowarsa daga Saudiyya, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kama hanyar tafiya birnin Glasgow na Scotland ranar Lahadi.

Shugaban ya yi balaguron ne domin halartar taron sauyin yanayi da aka yi wa lakabi da COP 26, inda zai haɗu da takwarorinsa na ƙasashen duniya.

Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar, Garba Shehu ya aike wa manema, ta ce sai a ranar Talata Buhari zai gabatar da nasa jawabin a wurin taron sannan kuma zai bayyana irin matakan da ƙasarsa ke ɗauka wajen rage ɗumamar yanayi.

Ana sa ran shugaban zai gana da shugaban Amurka Joe Biden da kuma na Faransa Emmanuel Macron.

Taron sauyin yanayin da aka yi wa lakabi da COP 26, taro ne da Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya kuma shugabannin kasashen duniya za su halarta domin duba ina aka kwana game da irinsa na baya da aka gudanar da birnin Paris a shekarar 2015.

Shugaba Buhari zai samu rakiyar wasu daga cikin kusoshin gwamnatinsa.

Sanarwar ta Malam Garba Shehu ta kara da cewa Shugaba Buhari zai nausa kasar Faransa domin halartar wani taron kan zaman lafiya da za a yi a birnin Paris.

Balaguron na shugaba Buhari na zuwa ne kwana biyu bayan ya dawo daga Saudiyya, inda ya halarci wani taron kan zuba jari sannan kuma ya gudanar da aikin Umrah

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...