Samar da jamia’ar MAAUN da Farfesa Adamu Gwarzo ya yi ya fitar da Arewa kunya – Murtala Iliyasu

Date:

Daga Bilyaminu Sani

Shugaban kwalejin kimiyya da fasaha na Arewa Ambassador International College Health science and Technology zariya malam Murtala iliyasu ya bayyana cewa samar da jamiar Maryam Abacha American university da farfesa Adamu Abubakar Gwarzo yayi ya fitar da Arewa kunya daga karancin masu ilimin kimiyya da fasaha da ta tsinci kanta a shekarun baya,

Malam Murtala Iliyasu ya bayyana haka ne Jim kadan bayan kammala ziyarar Gani da ido da Daliban kwalejinsa ta Arewa Ambassador zariya suka kai haraban ginin jamiar ta Maryam Abacha American University Nageriya dake Hotoro GRA a Birnin kano don sada zumunci da kulla Alaka

Shugaban na Arewa Ambassador ya kara da cewa kafin samar da jami’o’in MAAUN yankin Areawancin Nigeriya yana fama da karancin masu ilimin kimiyya da fasaha kwarai matuka, yace amma cikin yaddar Allah samar da jami’on MAAUN da Farfesa Gwarzo yayi ya kawo karshen waccan matsalar don haka babu abin da zamu ce sai godiya ga Allah da ya kawo wannan bawan Allah a yankin mu na Arewa

Malam iliyasu ya cigaba da cewa babu wani Baban Asibiti ko wata cibiya ta kula da lafiya a Nigerian da bazaka samu wani Dalibin jamiar Maryam Abacha American University dake Niger ba, wannan ba karamin babban abin Alfahari bane a daukacin duk wani mai son cigaban kasarmu Nigerian

“ mun zo Jami’ar Maryam Abacha American University dake Kano mun ga irin na mijin kokari da akayi wajen samar da ingantatun kayan aikin da aka tanada wajen koyar da Dalibi , Don haka muna shawartan iyaye masu neman wa ‘ya’yansu ingantaccen ilimin jami’a da su hanzarta kawo su MAAUN, Gini da kayan aiki sai kace a kashen Turai “ cewar iliyasu zariya,

Shugaban kwalejin Arewa Ambassador ya kammala bayaninsa da cewa a matsayinsu na yan birnin zazzau suna Jinjina da Godiya ga Farfesa Adamu Gwarzo kan yadda bai tsaya ga jihar kano ba, ya tsallako jiharmu ta kaduna ya zo ya samar mana da jamiar Franco British International University Kaduna, Muna godiya kwarai da Gaske, Allah ya karo mana yawaitan mutane masu kishi irin Gwarzo. A cikin mu,

Daliban na Arewa Ambassador A yayin ziyaran kwamaret Ali yusuf kakaki Ya zagaya da wasu wurare a cikin Jami’ar da ya haka da ginin Hukumar Gudanarwa, ajujuwan karatu, dakunan gwaje-gwaje, gidajen ma’aikata, dakunan kwanan dalibai da dakin karatu da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...