Daga Zainab Muhd Darmanawa
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya shiga jerin musulmi 500 masu karfin fada aji a fadin duniya.
Cibiyar nazarin addinin musulunci da ke kasar jodan ita ce ta bayyana hakan cikin Wani rahoto da ta wallafa bayan kammala bincikenta akan Mutane Musulmi Masu karfin fada aji a duniya.
Dama duk Shekara Cibiyar ta kan wallafa sunayen fitatun musulmi 500 masu karfin fada aji a duk duniya.
A banama Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya samu shiga cikin jerin sunayen a bangaren mayan malamai masu yin wa’azi.