Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya Nimet, ta yi hasashen cewa za a yi zafin rana da kuma tsawa daga ranar Juma’a har zuwa Lahadi.
A bayanin hasashen da ta fitar a ranar Alhamis a Abuja babban birnin ƙasar, Nimet ta ce za a ƙwalla rana a yankin arewaci a ranar Juma’a da kuma yiwuwar yin tsawa a wasu yankunan Taraba da safiyar Juma’ar.
Sannan hukumar ta ce ana sa ran za a yi ta jera tsawa a Adamawa da Taraba da kuma kudancin Borno a yinin ranar.
“Hadari zai yi ta haɗuwa amma rana za ta dinga fitowa jifa-jifa a yankin arewa ta tsakiya tare da yin tsawa a wasu yankunan jihohin Filato da Nasarawa da Neja da Binuwai da kuma Abuja da rana da yamma,” a cewar hukumar.
Ta kara da “Hadari zai yi ta haɗuwa a biranen da ke kusa da gaɓar teku ama ba za ayi tsawa ba a jihohin Ogun da Akwa Ibom da safiyar.”
“Can da rana kuma ana sa ran za a yi ta tsawa a wasu yankunan jihohin Imo da Abia da Ebonyi da Osun da Lagos da Rivers da Bayelsa da Delta da Cross River da kuma Akwa Ibom,” a cewar Nimet.
Sanarwar Nimet ta kuma ce ana hasashen za a ƙwalla rana a arewaci tare da yiwuwar yin tsawa da safe a yankunan jihohin Adamawa da Taraba da Borno da Yobe da kuma Jigawa ranar Asabar.
Sannan za a yi tsawa a biranen Kano da Kaduna da Katsina da Zamfara da SOkoto da Kebbi da Bauchi da rana da yamma.