Gwamnatin Kano tafi ta tarayya bada fifiko ga bangaren Lafiya – Dr. Tsanyawa

Date:

Daga Nafisa Abdullahi Diso
 Gwamnatin jihar Kano ta ware kashi goma sha bakwai na jimillar kasafin kudin ta domin farfado da kuma inganta sashin kiwon lafiya a jihar, sabanin amincewa da kashi goma sha biyar da gwamnatin tarayya ke bayarwa gaba daya.
 Kwamishinan lafiya, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa, shi ne ya bayyana hakan yayin rufe wani taron kwana biyu da aka shirya don ci gaban tsarin aikin rigakafin yau d kullum na Shekarar 2022 na Hukumar Kula da Lafiya matakin farko.
 Dakta Tsanyawa wanda ya bayyana irin nasarorin da gwamnati ke samu a fannin kiwon lafiya, ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba da fifiko ga bangaren ta hanyar bayar da duk abubuwan da suka dace ga cibiyoyin kiwon lafiya a jihar.
 Cikin Wata sanarwa da Jami’in hulda da Jama’a na Hukumar Maikudi Muhd Marafa ya aikowa Kadaura24 ya yabawa hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar bisa jajircewa wajen shirya taron.
 A nasa jawabin, Babban Sakataren Hukumar, Dakta Tijjani Hussain, wanda Daraktan Gudanarwa da harkokin Kudi na Hukumar, Alhaji Suleiman Tanimu ya wakilta, ya bayyana godiya ga gwamnatin jihar saboda jajircewarta na inganta sashin kula da lafiya a matakin farko.
 Sakataren zartarwa ya yabawa mahalarta taron da Masu bada tallafin don gudummawar da suka bayar wajen gudanar da taron cikin nasara.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta yanke hukunci kan ko ICPC tana da ikon gudanar da binciken kudin tallafin karatu na Kano

Babbar Kotun tarayya dake Babban Birnin Tarayya (FCT), karkashin...

Dalilan Hukumar tace fina-finai ta Kano na haramta muƙabalar tsakanin masu waƙoƙin yabon Ma’aiki S A W

Hukumar Tace Fina-finan Jihar Kano ta sanar da haramta...

‎Kawu Sumaila ya binciko kudaden da gwamnatin tarayya ta turawa kananan hukumomin Kano

‎ ‎Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu...