Muna nan akan bakarmu Kan saka dokar ta baci a Anambra-Lai Muhd

Date:

Gwamnatin Najeriya ta sake jaddada matsayarta game da yunƙurin saka dokar ta-ɓaci a Jihar Anambra saboda tashe-tashen hankali.

Tun a ranar Laraba ne Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana cewa “za mu iya saka dokar ta-ɓaci idan aka ci gaba da kashe rayukan al’umma” jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa wanda Shugaba Buhari ya jagoranta.

Da yake magana da kamfanin labarai na NAN ranar Alhamis, Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ya ce Malami ya bayyana hakan ne domin kauce wa rikicin kundin tsarin mulki.

“Ministan shari’a ya faɗa cewa gwamnati za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen dawo da doka da oda a Anambra da dukkan yankin kudu maso gabas don ganin cewa ba a yi wasa da turakun dimokuraɗiyya ba,” in ji shi.

“Zaɓen gwamna da za a yi ranar 6 ga watan Nuwamba yana cikin turakun dimokuraɗiyya.”

Kazalika ministan ya zargi ƙungiyar ‘yan tawaye ta IPOB da hana mutane zuwa makarantu da kasuwanni a jihar.

“IPOB ta saka dokar hana fita a ‘yan makonnin da suka wuce. Sun hana mutane zuwa makarantu da kasuwanni da kuma kashe manyan mutane.

“Masu sukar ministan shari’a game da kalamansa, sun taɓa yin tunani ko na minti ɗaya game da abin da zai faru idan ba a samu damar yin zaɓe ba a Anambra ranar 6 ga Nuwamba?”

An kashe mutane da dama a Anambra cikin ‘yan makonnin na da suka wuce, ciki har da ‘yan siyasa da ma’aikatan gwamnati yayin da ake shirin gudanar da zaɓen gwamnan jihar ranar 6 ga Nuwamba.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tsofaffin Kansiloli Sun Yi Saukar Alƙur’ani da Addu’a na Musamman ga Gwamna Abba

  Ƙungiyar tsofaffin kansiloli na jihar Kano ta gudanar da...

Hisbah ta kama mutane 25 bisa zargin shirya auren jinsi a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama akalla mutane...

Yadda ƴansanda suka kama wasu da suke zargin ƴanbindiga ne a Kano

Rundunar yansanda ta Kasa reshen jihar Kano ta ce...

Rikici a Bebeji: Jigon Kwankwasiyya na zargin an shirya cire sunayen tsoffin kansiloli domin yin kashe-muraba

Wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya a karamar hukumar Bebeji...