Daga Halima M Abubakar
Shahararren mawakin Hausa Magajiya Danbatta ta rasu tana da shekaru 85 a duniya.
Dangane da Wani rubutu da tsohon manajan daraktan Rediyon Kano, Adamu Salihu yayi akan wakokinta, ya bayyana yadda ɗaya daga cikin waƙoƙin ta ta bayar da Gudummawa wajen shigar da yara makaranta a farkon shekarun 1970 Inda akai nasarar sanya ɗalibai sama da 3,000 a Kano Sakamakon wakar data yi.
“Na yi imanin wasu daga cikin ɗaliban, waɗanda waƙarta tasa iyayensu Suka Kai su makaranta, yanzu Haka sun Zama farfesoshi.
A shekarar da ta gabata, editan Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, ya bayyana yadda take shan wahala kuma ya sami nasarar samar da kuɗin da aka Gina Mata gida da Kuma Samar Mata na cefane don kyautata Rayuwar ta.
Веном 2 – смотреть онлайн в хорошем качестве https://bit.ly/venom2-2021