Sama da kaso 17 cikin 100 na barayin internet Yan Nigeria ne – Abdallah Uba

Date:

Daga Sani Magaji Garko

Kwararre a Bangaren ilimin kimiyya kuma tsohon shugaban jami’ar Karatu daga Gida NOUN Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce kididdiga ta nuna cewa sama da kaso 17 cikin 100 na Yan damfarar internet ‘yan Nigeria ne.

Abdallah Uba Adamu ya bayyana hakan ne cikin wata takarda da ya gabatar akan aikata lefuka a internet wacce kungiyar tsofaffun daliban makarantar sikandiren Gwale GOBA ta shiryawa daliban ajin karshen na makarantar taron da ya gudana a harabar makarantar.

Abdallah Uba Adamu wanda Kuma kwararre ne a bangaren sanadarwa da kuma al’adu ya ce a yanzu haka ana gudanar da lefuka a internet, Wanda hakan ne yasa aka wayar da kan al’umma musamman dalibai da matasa matsalolin da lefukan internet kan haifar musamman wajen kawo nakasu a cigaban kasa.

“Wasu daga cikin ayyukan da mukeyi, muke ganin ba laifi ba ne amma kuma laifi ne a doka. Sauko da litattafai da wakoki da hotuna masu motsi ba tare da izini ba dukka lefi ne. Matukar kayi amfani da kayan mutum ba tare da izini ba lefi ne” Inji Shi.

Ya ce taron ya mayar da hankali ne wajen wayar da kan daliban makarantar sikandiren Gwale yadda zasu kare kansu daga Yan damfarar internet da kuma illarsa ga tattalin arzikin kasa.

Farfesa Abdallah Uba Adamu daga nan ya bukaci al’umma da su kasance masu bin ka’ida wajen mallakar kayayyakin amfanin yau da kullum ko a internet ko akasin haka.

A jawabinsa, shugaban kungiyar ta GOBA Injiniya Hassan Abdulqadir ya ce an shirya taron ne domin wayar da kan daliban makarantar sikandiren Gwale yadda ayyukan damfarar internet ta ke da kuma yadda zasu kare kansu.

Injiniya Hassan Abdulqadir ya ce an koyawa daliban hanyoyin kirkire-kirkire da harkokin noma domin su zamo masu dogaro da kansu.

A nasa bangaren
, Shugaban Hukumar Kula da Makarantun sikandiren jihar Kano Dakta Bello Shehu ya ce shirya taron ya zo dai-dai a lokacin da ake bukata laakari da matsalolin damfarar internet da ake fuskanta yanzu.

Dakta Bello Shehu Wanda Umar Muhammad Yakasai ya wakilta ya ce tuni sun fara tuntubar farfesa Abdallah Uba Adamu domin shirya irin wannan mukalar ga sauran Makarantun sikandiren jihar Kano.

Ya ce “Matasa a yanzu suna da kaifin basira saboda haka mutakar su ka shiga damfara a internet to dole al’umma da wahala.

Kadaura24 ta rawaito cewa dangane da bukatar shirya irin wadannan mukala a sauran Makarantun sikandiren da aka zo da ita kuma, da ma hukumar kula da Makarantun sikandiren jihar Kano karkashin jagorancin Dakta Bello Shehu na kan shirya ire-iren wadannan ayyukan Kuma sashen da nake kula dashi ne ke da alhakin horar da Malamai da dalibai a don haka zamu tabbatar dukkan daliban jihar Kano sun amfana da irin wadannan makaloli”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...