Yada hotunan Zara Beyero Haramun ne – Hukumar Hisbah

Date:

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da ke ta yi kira ga masu yada hotunan ‘yar Sarkin Bichi, Zarah Nasiru Ado Bayero wadda Dan shugaban kasa Yusuf Buhari zai aura, da su guji yin hakan “saboda ya saba wa Shari’ar Musulunci”.

Kwamandan Hisbah Harun Muhammad Ibn-Sina ya ce aikin hukumar shi ne hana yada barna ko da kuwa ta faru a baya, ba wai “tonowa da kuma hukunta mutum ba”.

Kiran na Hisbah ya biyo bayan dubban ra’ayoyi da mutane suka dinga bayyanawa a shafukan zumunta cikin kwana uku da suka wuce bayan hotunan amarya Zarah sun karaɗe shafukan sanye da wata doguwar riga.

A cikin hotunan wadanda ba a gan ta tare da angon ba, babu dan kwali a kan gimbiyar ta Masarautar Bichi da ke Kano sannan kuma saman rigar yana da launin fatar jikinta.

Wasu bayanai sun ce hotunan sun ɓulla ne daga wani bikin mata zalla da aka gudanar a Abuja a wannan makon.

Wannan ne ya sa masu amfani da shafukan zumunta suka dinga kira ga Hisbah da ta ɗauki mataki, inda sunan hukumar ya kasance daya daga cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a kafofin na Najeriya tun daga ranar Laraba zuwa Juma’a.

Hukumar Hisbah ta Kano wadda aka sani da tabbatar da bin dokokin Musulunci, ta ce yada hotunan “ya saɓa wa Shari’ar Musulunci”.

Cikin wata hira da manema labarai, Kwamandan Hisbah Harun Muhammad Ibn-Sina ya ce ba aikin hukumar ba ne tonowa tare da kama masu laifi, aikinsu shi ne hana yaɗa ɓarna.

77 COMMENTS

  1. Allah sarki talaka babu inda doka take aiki sai akan talaka dan Yanzu da talaka ne yayi wannan aikin Da tuni an kama a halinsa amma saboda masu kwali a idone babu abunda zai fara
    Kukan kuciya jawabe ne

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta ɗaure wani ɗan Tiktok mai wanka a tsakiyar titunan Kano

    Wata kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya...

Damuna: Mun shirya inganta wuraren tsayarwar motocinmu – Kungiyoyin Direbobin na Kano

Kungiyar matuka motocin kurkura ta jihar Kano da Kungiyar...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ba ga Nigeria kadai ba – Mustapha Bakwana

Daga Zakaria Adam Jigirya   Tsohon Mai baiwa gwamnan Kano shawarawa...

Gwamnatin Kano ta yabawa Tinubu saboda gyarawa da bude NCC DIGITAL PARK

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin jihar Kano ta yabawa Gwamnatin...