Inganta Tsaro: Doguwa ya bada Gudunmawar motoci da gina ofishin Yan Sanda a Yankinsa

Date:

Daga Zainab Muhd Buhari

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da kwamitocin Yan Sanda da al’umma na masarautar Rano .

Yayin da yake kaddamar da kwamitocin Wanda suka kunshi na matakan mazabu dana kananan hukumomi goma dake masarautar ta Rano Wanda aka gudanar a karamar hukumar tudun wada, gwamna ganduje ya ce kwamitocin zasu Rika taimakawa gwamnati da Jami’an tsaro a duk lamuran da suka Shafi tsaro.

Yace kwamitocin zasu Rika Zama a kowanne Wata domin Tattaunawa tare da mika Rahoton su ga babban Kwamitin na jiha Dake karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin jiha.

Gwamna Ganduje yace yan kwamitin sun kunshi jamian yan sanda yan bijilante yan Hisbah, limaman masallatan juma’a da sanannu Mutane, shugabannin dalibai, da Kungiyoyin da suke Cikin al’umma da dai Sauransu.

Ya Kuma bukaci Kamfanoni da Masu Rika da madafun ikon dasu tallafawa Shirin domin Samun nasarar da ake fata.

Yayin da yake Mika sabbin motocin ga hukumar yan sanda da sojoji da yankarota tare da bude sabon ofishin yansanda da Dan majalisa Alasan Ado ya samarwa kwamitin tsaron, gwamna Ganduje ya bukacesu dasu yi amfani da motocin wajen Kara karfafa tsaro a yankin masarautar duba da yadda suke makwaftaka da Wasu jihohin Nigeria.

Da yake Jawabinsa Dan majalisar mai wakiltar Kananan Hukumomin doguwa da tudun wada Alhasan Ado Doguwa ya yabawa kokarin gwamnatin jaha tare da hadin kan gwamnatin tarayya na mayar da dajin falgore sansanin horar da sojoji Wanda hakan ya inganta tsaro a yankin masarautar Rano dama jahar Kano baki daya.

Alhassan Ado yace ya bada Gudunmawar motocin ne har guda 6 domin taimakawa yunkurin gwamnatin jihar Kano na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Mai Martaba Sarkin Rano Alhaji Kabiru Muhammad inuwa ya bada tabbacin bada cikakken hadin kai ga kwamitin domin sauke nauyin da aka daura musu.

Bayan kaddamar da kwamitocin Gwamnan ya jagoranci Bude ofisoshin Yan Sanda dana karota Waɗanda Alhassan Ado Doguwa ya masar a Karamar Hukumar Doguwa.

A Wani labarin Kuma Gwamnan Ganduje ya Ziyarci Garin Doguwar giginya dake Karamar Hukumar ta Doguwa don yin ta’aziyya ga iyalan Mutane 18 da Suka Suka rasu Sakamakon ambaliyar Ruwa tare da basu tallafin Naira dubu dari 2 kowannensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...