Daga AB Kaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ceto dalibai biyu daga cikin daliban da aka sace na kwalejin Birnin Yauri a jihar Kebbi.
Kadaura24 ta rawaito Kwamishinan ‘yan sanda na rundunar,CP Hussaini Rabiu ya baiyana haka yayin ganawarsa da manema labarai a hedikwatar’ yan sanda da ke Gusau ya ce an ceto daliban ne a kauyen Babbar Doka da ke gundumar Dansadau a karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
“Ma’aikatan mu na Operation zaman lafiya sun yi nasarar kubutar da dalibai biyu wato Maryam Abdulkareem ‘yar shekara 15 a karamar hukumar Wishishi ta jihar Neja da Faruk Buhari dan shekara 17 na karamar hukumar Wara ta jihar Kebbi lafiya a Kauyen Doka a gundumar Dansadau ”inji CP Hussaini .
Kwamishinan ya yi bayanin cewa, an kai daliban asibiti domin duba lafiyarsu kuma ‘yan sanda suna kara samun bayanai Daga Daliban.
Lura da cewa, za a mika daliban ga rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi don ci gaba da daukar matakan da suka dace tare da mika su ga Iyayen su.
Wasu daga Cikin yan uwan daliban da aka sako wadanda suka halarci taron manema labaran sun nuna farin ciki tare da nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da Kuma kokarin ‘Yan Sandan.