Ministan albarkatun Ruwa na Kasa Engr. Sulaiman Adamu kazaure ya Mika Rijiyoyin burtsatse Mai Amfani da hasken Rana guda 6 wadda gwamnatin tarayya ta Samar a garuruwan Gwaleda, Kuku, agalawa, Baje, madaka, da Kuma Garin rigana duk a Karamar Hukumar Kunchi Dake nan jihar Kano.
Ministan Wanda Injiniyan daya gudanar da Aikin Engr. Maina Rabi’u ya wakilta ,ya Mika Rijiyoyin ga al’ummar garurun tare da koya musu yadda zasu yi amfani dasu da Kuma yadda zasu kula da Rijiyoyin ba tare da Wata matsala ba a Garin Gwaleda Dake Karamar Hukumar.
Engr. Maina Rabi’u yace makonni biyu da Suka gabata Minista Sulaiman Adamu ya je har Karamar Hukumar Kunchi domin kaddamar da Aikin Rijiyoyin burtsatsen Saboda kokarin Shugaban Kasa Muhd Buhari na Kawo Karshen karachin Ruwan Sha wanda aka gudanar su karkashin Shirin inganta Ruwan Sha da Tsaftace shi tare da Magance Matsalar Ruwan da aka Dade ana fuskanta a yankin.
Engr. Maina ya Kuma yaba da Gudunmawar da Hukumar Ruwasa ta bayar Yayin da ake gudanar da Aikin, tare Kuma da yin Kira ga al’ummar da su baiwa Rijiyoyin burtsatsen kulawar data dace domin su Jima Suna Amfana.
Da yake Jawabin godiya a madadin al’ummar garuruwan da Suka Amfana da Rijiyoyin burtsatsen Malam Dauda Inuwa Gwaleda ya yabawa Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin jihar Kano bisa kokarin da sukai na Magance musu Matsalar Ruwan da Suka dade Suna fama da ita.