Majalisar Dokokin Kano ta bukaci a kama Muhuyi Magaji

Date:

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ba da shawarar kora tare da kame Dakataccen shugaban Hukumar karbar korafe-korfen da hana da cin hanci da rashawa na jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado ba tare da bata lokaci ba.

An gabatar da wannan kudurin ne a lokacin zaman majalisar wanda Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya jagoranta.

Yayin gabatar da rahoton, shugaban kwamitin wucin gadi Wanda Majalisar ta kafa Alhaji Umar Musa Gama ya bayyana cewa kwamitin Mai mambobi 12 sun kammala bincike kuma sun tsara shawarwari 5 da za a gabatar.

Ya yi nuni da cewa shawarwarin sun hada da korar shugaban da aka dakatar nan take, kamawa da gurfanar da Muhyi tare da kafa wani kwamiti na wucin gadi da zai binciki ayyukan kudi na Hukumar karbar korafe-korfe da yaki da cin hanci da rashawa daga shekarar 2015 zuwa yau.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan zaman, shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhaji Labaran Abdul Madari ya ce kwamitin hadin gwiwar da majalisar ta kafa don binciken Muhyi ya gano cewa rahoton likitan da lauyan shugaban da aka dakatar ya gabatar karya ne.

Ya lura cewa kwamitin ya kuma ba da shawarar cewa Shugabar ma’aikatan gwamnati ta jiha ta dauki matakin da ya dace a kan Isah Yusif wani jami’i Mai Matakin albashi na hudu da ke aiki a matsayin akawu a hukumar karbar korafe-korfen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.

Alhaji Labaran ya ce kwamitin ya kuma yi kira ga akawun da Muhyi ya ki amincewa da shi daya fara aiki da wuri-wuri a Hukumar.

Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa majalisar dokokin jihar Kano ta karbi korafi daga ofishin babban akawun jiha game da kin amincewa da wani babban akawun da aka dakatar da shi da shugaban da aka dakatar ya tura

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...