Daga Abubakar Sa’eed
Jam’iyyar PDP a Kano karkashin jagorancin shugabanta Shehu Wada Sagagi ta kafa wani kwamitin ladabtarwa da zai binciki Dokta Yunusa Adamu Dangwani da Yusuf Bello Dambatta.
An dai kafa kwamitin ne bayan Wani korafi da wani Ahmed Sani Maidaji Daga yankin Dambatt ya rubuta a kan Yusuf Bello Dambatta.
Dr. Yunusa Adamu Dangwani ya bayyana a gaban kwamitin da jam’iyyar ta kafa domin amsa tambayoyi kan zargin yi wa jam’iyyar zagon kasa da jagoranta Sen. Rabiu Musa Kwankwaso a ranar Alhamis.
Dangwani wanda ake ganin shi ne na biyu a tafiyar Kwankwasiyya ya samu sabani da dan takarar gwamnan Kwankwaso a zaben 2019 Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida.
Ba Dangwani kadai ba, ana gani Abba bashi da kyakykyawar alaka da akasarin masu ruwa da tsaki na Kwankwasiyya kamar yadda suka zarge shi da rashin mutunta su duk da kasancewarsu Kwamishinoni da mataimaka ga jagoransu Kwankwaso.
Mutum na biyu da ya bayyana a gaban kwamitin a ranar Laraba shi ne Yusuf Bello Danbatta, ya kasance tsohon kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki kafin a sauya shi zuwa Ma’aikatar Kasa da Tsare-tsare, daga baya kuma ya yi wa Sanata Kwankwaso aiki a matsayin Mataimaki na Musamman a Majalisa ta 8.
Dambatta shi ne kwamishina mafi karancin shekaru a wa’adin mulkin Kwankwaso na biyu.
Kwamitin Mai mambobi 7 da jam’iyyar ta kafa sun nemi mutanen biyu da su mayar da ba’asi kan zargin Suna da hannu a Fastocin da aka yada a shafukan sada zumunta dauke da hotunan wasu masu ruwa da tsaki na tafiyar Kwankwasiyya mai taken “Restoration Team 2023” da kuma wata waka wacce Har ila yau ta yadu inda mawaƙin yake cewa “Ya kamata a ba Dangwani tikiti ko kuma jam’iyyar ta tarwatse”
An watsa wakar a dandamalin sada zumunta kuma ta haifar da musayar kalamai tsakanin magoyan bayan Abba Kabir Yusuf da Dr Yunusa Dangwani.
Politics Digest ta rawaito cewa ta samo wani labarin sirri da ke cewa Kwankwaso ya umarci kwamitin da ya bayar da shawarar korar Dangwani da Bello Dambatta daga jam’iyyar a rahotonsu na karshe.
Membobin kwamitin sun hada da:
Hashimu Dungurawa
Dahiru Kibiya Dakata
Hafiz Bunkure
Bintoto Kofar Ruwa
Halima Uba Jalli
Jamilu Kabo da Barista Wangida a matsayin Sakataren kwamitin.
Lamarin dai duk ya faru ne a gidan Sen. Rabiu Kwankwaso a ranar Alhamis.
Jaridar Politics Digest tayi Kokarin jin ta bakin shugaban jam’iyyar Shehu Wada Sagagi game da lamarin Amma hakan bata ba domin bai amsa kira da sakon tes da wakilinsu ya aika masa ba.