Daga Amira Sanusi
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya amince da nadin Barista Mahmoud Balarabe, wanda a halin yanzu shi ne Darakta na Mai lura da shigar da kara na Ma’aikatar Shari’a ta jihar, a matsayin mukaddashin Shugaban Hukumar karbar karbar korafe-karafe da yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano.
Sanarwar nadin na dauke ne Cikin wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran gwamna Malam Abba Anwar ya aikowa Kadaura24.

Sanarwar nadin ta fara aiki nan take kuma Gwamna Ganduje ya umarci mukaddashin Shugaban Hukumar da ya gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, bisa ga tsarin da dokar da aka kafa Hukumar akai