Rikici Kan Gona : An hallaka wani Dagaci har lahira a kano

Date:

Daga Halima M Abubakar

Wani dattijo mai shekaru 45 a duniya a garin Zananne dake karamar hukumar Albasu ta jihar Kano, Bashir Adamu Abdullahi ya gamu da ajalinsa a hannun wani mai suna Sale Yusuf Gamboni mai shekaru 45 Wanda yayi Amfani da wuka ya kashe shi saboda zargin rikicin gona

Da yake ba da labarin abin da ya faru ga Majiyar Kadaura24 Justice Watch News wani dan uwansa Mamacin Usman Baffa Shitu ya ce mummunan lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 3 ga watan Yulin, 2021 da misalin karfe 900hrs

“rashin fahimta ne kan burtali shanu da ke gefen gonar Sale Yusuf Gamboni.” A cewar sa

Ya bayyana cewa tun farko, Dagacin Bashir Adamu ne ya dasa shuka a kan hanyar shanu kusa da gonar Salisu kuma da ya zo washegari da safe sai ya lalata dukkanin shukar.

Baffa ya ci gaba da bayanin cewa Dagacin sai ya tafi wajen salisu din Jin dalilin da yasa ya lalata Masa shukar da yayi .

”Hakan ta fusata Salisu kuma ya fito da adda ya dabawa Dagacin a fuska bayan ya Fadi Kasa Kuma ya bishi ya caka masa addar a tsakiyar bayan sa .

Yayin haɗa Wannan rahoton salisu ya gudu ba a san Inda yake ba.

A nasa martanin, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan ta kano DSP Abdullahi Haruna ya ce bai sami labarin faruwar lamarin ba amma yace zai yi bincike akai.

166 COMMENTS

  1. Олександр Усик і Ентоні Джошуа вийдуть на ринг 25 вересня в Лондоні, на арені стадіону “Тоттенгема” Українець спробує відібрати у британця пояса wba, wbo, ibf і ibo в суперважкій вазі. Для Усика майбутній бій стане третім у Джошуа Усик дивитися онлайн Усик зможе перемогти Джошуа за однієї умови, — експерт з боксу. За інформацією джерела, Джошуа за бій з небитих українцем отримає гонорар у розмірі 15 млн фунтів стерлінгів. Дана сума на 50%

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...