Mutuwa ce Kadai zata rabani da Siyasa- Mal Shekarau

Date:

Daga Nura Abubakar

Tsohon Gwamnan jihar kano Sanata Malam Ibrahim Shekarau (Kano ta Tsakiya) ya sha alwashin ba zai yi ritaya daga siyasa ba har mutuwa ta zo ta riske shi.


 Mal Shekarau ya shaida wa manema labarai a ranar Lahadi cewa “Ba ni da lokacin da zan yi ritaya daga siyasa har sai na mutu.”


 Ya yi bayani game da makomar siyasarsa jim kaɗan bayan ya kaddamar da Majalisar Shura wacce Zai Rika Amfani da ita wajen karbar shawarwarin magoya bayan Kan duk Wata matsaya da za’a dauka a siyasance.


 Ya ce: “A zahiri, dalilin da ya sa na sake dawowa don yin magana a karo na biyu shi ne yin sabani a wannan bangaren.  Ni dai kamar yadda na damu, babu lokacin da zan yi ritaya daga siyasa.


 “Ina fadin wannan tun shekaru 20 da suka gabata.  Siyasata addinina, siyasa ta kuma babu lokacin yin ritaya domin na dauke ta addinina tun da tare suke tafiya.


 “Addini shi ne bautar Allah ne kuma kololuwar bautar Allah ita ce bauta wa dan Adam wadanda halittun Allah ne.


 “Idan na wuce shekaru 90 ko kuma na tsufan da bazan iya tsayawa takara ba ko fita yaki neman Zabe,Daga Kan Gado na zan rika ba da shawara ga al’umma da Kuma abokan siyasa ta ,Siyasa hanya ce ta yiwa dan Adam hidima, wannan ita ce fahimtata.


 Ya kara da cewa: “Fahimtata da siyasa ita ce damar yin hulda da jama’a da kuma yiwa‘ yan adam hidima ta kowace fuska.

Don haka bani da Wani lokacin yin ritaya a Siyasar “Na fadi haka ne saboda akwai jita-jita da wasu suke yadawa Waɗanda watakila abokan hamayya na ne, sun na karya cewa Wai Zai daina Siyasar, watakila sun yi haka ne Saboda sagarwa da magoya bayan mu gwiwa cewa Sardaunan Kano (Shekarau) zai yi ritaya nan ba da jimawa ba”.

65 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Amfani da al’ada a cikin fina-finan kannywood ne ya hana masa’antar ci gaba – Khadija Osi

Jaruma a masana'antar Kannywood Khadija Muhammad wacce aka fi...

Nasarar da Ɗaliban Kano suka Samu a NECO Kokari ne na Gwamnatin Ganduje – Sanusi Kiru

Tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Hon. Muhammad Sanusi...

Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Aikin samar da wutar sola na Naira Biliyan 12 a asibitin Malam Aminu Kano

Kwana biyu bayan rikicin wutar lantarki tsakanin Asibitin Koyarwa...

Kano Ta Zama Zakara A Jarrabawa NECO Ta Bana

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta Najeriya (NECO),ta fitar...