Burina na Duniya ya Gama kammala-Sarkin Kano

Date:

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce babban burinsa a rayuwa shi ne ya gaji magabatansa kuma yanzu hakan ya tabbata.

Cikin wannan hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa, sarkin ya ce baya ga murnar gadar mahaifinsa da yake yi yana kuma murnar zaɓarsa da Allah ya yi domin ɗora masa nauyin taimaka wa al’ummarsa.





Ya bayyana haka ne yayin da ake shirin bikin ba shi sandar girma, yana mai cewa a halin yanzu murna biyu yake yi.

Kazalika sarkin ya bayyana cewa babu wata tashin jituwa tsakanin ‘yan gidan sarautar Kano.

A cewarsa a al’adance duk wanda ya nemi wani abu bai samu ba ba zai ji dadi ba amma hakan ba ya nufin akwai rashin matsala tsakaninsa da wadanda ya gada da wadanda suka nemi mulki tare

72 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...