An yi dokar takaita kayan aure a garin Aujara

Date:

Daga Tijjani Mu’azu Aujara

Masarautar Aujara dake Karamar Hukumar Jahun ta jihar Jigawa sun Dauki matakan saukaka al’amuran da suka shafi aurataya a yankin.

Dan Malam din Dutse Hakimin Aujara Alh Aminu Dan malam Muhd ne ya jagoranci kaddamar da dokar kyautata al”adun auratayar ta garin Aujara.

Hakimin ya bayyana cewar dokar zata taimaka sosai wajen rage yawan Yan Matan da ake da su a Garin na aujara.

Dokar dai tayi bayani dalla-dalla Kan yadda Dokar zata kasance Kamar haka kayen aure [lefe] Akwati 1, zannuwa kala 10, sauran kayayyaki biyu – biyu tare da kudin toshi da gaisuwa N 20,000 kacal.

Hakimin ya Kuma ce Dokar ta Hana zance ga samari da yan Mata da daddare sai dai da Rana zuwa magariba.

Anasa jawabin shugaban kwamatin Farfesa Idris Wada ya baiyana cewar kwamatin ya amince da yin gara buhu 1, taliya da macaroni guda 1-1 tare da yan kayen miya. a inda ya kara da cewar kwamatin ya soke kayen ango kayen uwar miji, DJ, da kuma Dane-dane da toye -toye.

Kadaura24 ta rawaito cewa dokar dai ana ganin zata sassautawa samari da Kuma Iyayen yaran wajen gudanar da aure.

23 COMMENTS

  1. Mash-Allah, Allah Ubangiji ya Kara hada kan al’ummar wannan gari namu Baki daya, ya Kuma bamu ikon yiwa wanna doka biyayya.

  2. Mash-Allah, Allah Ubangiji ya Kara hada kan al’ummar wannan gari namu mai albarka, kuma yabamu ikon bin wannan doka iya tsawon rayuwarmu dama masu zuwa bakidaya.
    Allah yayi mana jagoranci ameen. Sukuma wadda suka assasa wannan abin alkairi Allah yabasu lada yayi musu sakayya da gidan aljanna!! Ameen.

  3. Masha’Allah! Hakan yayi kyau sosai. Allah yasa sauran masarautun mu dake fadin wannan jiha suyi koyi da wannan abin akairi.

  4. Assalamu alaikum wannan ci gaba wanda al’umma zasuyi kiyi dashi. Amma ya kamata suma iyayen Amarya a tausaya musu. Yawanci zaka samu mutum mai karamin karfi yana da ‘ya’ya yanmata kamar biyar amma a auren guda daya zai sayar da gonarsa ta gado kuma tun daga nan ale shiga matsala. Yawa yawa kananan ma’aikatan gwamnati suna fadawa matsalar bashi sakomakon autar da yarinya, wani shi da warwarrwa sai yayi ritaya. Inaga ya kamata idan za’a sassauta matsalar a rika duba kowanne bangaren.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu a Benue

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi...

Rashin Jami’ar Mallakin jihar a shiyyar Kano ta Arewa na kokarin bayar da yankin baya – Alh. Mustapha Ahmad Gwadabe

Daga Shehu Hussaini Ahmad Getso An bukaci Gwamnatin jihar Kano...

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Almuharram a Nigeria

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji...

Yan uwan wata mata sun zargi Asibitin Malam Aminu Kano da sakaci wajen mutuwar yar uwarsu

Daga Sadiya Muhammad Sabo   Yan uwan wata mata da ta...