Hukumar Hizbah ta Jihar Kano ta haramta wa teloli da masu shaguna amfani da mutum-mitumi wajen tallafa samfuran ɗinkunan su, ko kayan sayarwar su.
Premium times ta rawaito kwamandan Rundunar Sheikh Haruna Ibn Sina ne ya bayyana haka, inda ya ce kafa mutum-mitimin mai kama da gunki, ya saɓa wa Musulunci.
A Kano dai yawancin teloli da masu kantinan sayar da kayan zamani su na amfani da mutum-mutumin roba, wanda ake sa wa kaya, domin kwastomomi su ka yadda samfurin suturar ke bin dirin-jiki.
Sai dai kuma daga ranar Laraba Hisbah ta yi hani ga yin amfani da su, kuma hukumar ta ce za ta fara bi shagunan teloli da kantinan sayar da kayayyakin zamani ta na kama duk wanda ya karya wannan doka.
Hukumar Hizbah dai tun farkon kafa ta ne ta haramta sha, sayarwa da safarar giya a fadin jihar