Neco: Ganduje ya Umarci Kananan Hukumomi su biyawa Dalibai 600 kudin jarrabawa

Date:

Daga Halima M Abubakar

An yi kira ga attajirai da kungiyoyi masu zaman kansu a jihar Kano da su hada hannu da gwamnati don farfado da martabar ilimi a jihar.


  Kwamishinan kananan hukumomi da lamuran masarautu Alh murtala sule Garo ya yi wannan rokon yayin da yake zantawa da manema labarai a jihar Kamar yadda Jami’in Hulda da jama’a na Ma’aikatar faruk Ghali Masanawa ya fitar da sanarwa.


 Alh murtala sule Garo ya ce gwamnan jihar Dakta Abdullahi umat Ganduje ya umarci kananan hukumomin guda takwas dake kwaryar Birnin Kano da su zabi daliban da suka Fadi jarrabawar qualifying guda 400 yayin da sauran ragowar kananan hukumomi 36 aka basu Umarnin su zabi dalibai 200 su biya musu kudin jarrabawar Neco.


Murtala Garo ya ce tuni gwamnatin jihar ta umarci karamar hukumar 44 a jihar da su kafa kwamiti domin zabo daliban da gwamnatin jihar za ta biya .


 Alh murtala sule Garo ya yi kira ga membobin kwamitin da su nuna dattako yayin gudanar da aikin binciken zabo Daliban da iyayensu ba za su iya biyawa ‘ya’yansu don rubuta jarabawar .


 Daga karshe kwamishinan ya bada tabbacin cewa gaba daya daliban da basu da gata 10,400 a jihar za su zauna a jarabawar su ta hannun gwamnatin Ganduje, don haka ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da ba Gwamna Ganduje goyon baya tare da yi masa addu’a kan kokarin da take yi na ganin ta inganta Ilimi a Kano

91 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...