Neco: Wani Dan Jarida a Kano ya Baiwa Ganduje Shawara

Date:

Daga Sayyada Ahmad Zage

Wani Dan Jarida dake gudanar da acikinsa a Wani gidan Radio a Kano Mai Suna Aliyu Safwan Alhassan ya shawarci gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Dangane da yadda za’a tallafawa Daliban da Suka Fadi jarrabawar qualifying.

Aliyu Safwan Alhassan Wanda ma’aikaci ne a Aminci Radio a Kano yace muddin Gwamna Ganduje ya bi Shawarar tasa za’a Sami mafita Kan batun da a Yanzu Haka yake ciwa Iyayen Dalibai tuwo a kwarya.

Ga Shawarar tasa

Aliyu Safwan Alhassan

Ina ma ace Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje yazo da wani tsari don taimakawa kannenmu da suka fadi a jarrabawar Qualifying.

Gwamna ya Kira masu rike da madafun Gwamnati don ta-da Wani asusun da za’a Tara Koda miliyan 200 ne ko sama da haka.

  1. Ministocin da muke dasu guda biyu kowanne ya bada miliyan 10.
  2. Accountant General na kasa ya bada miliyan 10.
  3. Masu rike da mukaman Siyasa a Matakin Tarayya gaba dayanmu ayi musu kudin goro su bada miliyan 10.
  4. Sanatocinmu guda uku kowanne ya bada miliyan 5.
  5. Yan Majalisun Tarayya kowannensu ya bada miliyan 2.
  6. Yan Majalisun Jiha kowanne ya bada naira dubu Dari 5.
  7. Kwamishinoni kowanne ya bada dubu dari 2.
  8. Shugabannin Kananan Hukumomi su gamayyarsu su hada miliyan 10.
  9. Attajiran Kano gaba dayansu a kai kokon bara su hada miliyan 100.

Na tabbatar idan Gwamna yayi haka, tunda ance Gwamnatin Babu kudi, na tabbatar za’a taimakawa kusan kaso 50% cikin kannenmu talakawa domin a biya musu kudin zana jarrabawar NECO.

Allah Yasa mu dace.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Na sauke nauyin da Tinubu ya ɗora min – Gwamnan riko na jihar Rivers

Vice-Admiral Ibok-Ete Ibas (Mai ritaya), wanda shi ne gwamnan...

Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi: Kawu Sumaila ya jinjinawa Gwamnan Kano

Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar...

Gwamna Yusuf Ya Shirya Baiwa Kananan Hukumomin Kano Cikakken ‘Yan cin Kai

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...

Majalisar Zartarwa ta jihar Kano ta Amince da kashe Naira Biliyan 18 don aiwatar da wasu aiyuka

  Majalisar zartarwar jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir...