Masu burodi sun kuka da tashin farashin Fulawa, sun nemi tallafin gwamnati

Date:

Daga Sani Danbala Gwarzo

Masu yin burodi a jihar Kano, a karkashin hadaddiyar kungiyar Masu sana’ar Biredi da dangoginsa ta Kasa reshen jihar Kano sun ce ƙarin farashin fulawa ya sa ba su da wani zaɓin da ya wife su ƙara farashin burodi don dorewar  kasuwancinsu a  jihar.


 Da yake Zantawa da manema labarai a Kano a ranar Juma’ar nan Sakataren kungiyar, Kabiru Hassan Abdullahi ya ce sun yanke shawarar ne saboda karin farashin fulawa da sauran abubuwan da ake amfani da su wajen yin biredin.


 A cewarsa, kungiyar na iya daukar matakin dakatar da sana’ar ko Kuma Kara farashin Burodin, amma yace Gudun kada dubunnan matasa dake cin Abinci da sana’ar wanda hakan zai iya zama barazana ga zaman lafiyar jihar, shi yasa suka yanke shawarar kara farashin Burodin a nan gaba. 


 Abdullahi ya zargi gwamnatin tarayya kan gazawar ta na amsa rokon su na shiga tsakani don kawo karshen matsalar.


 Ya ce kungiyar ta samar da ayyukan yi ga dubunnan matasa a jihar kano kuma tana bayar da gudummawa matuka wajen wadatar abinci a jiha, amma akwai matsalolin da suke fuskanta Wanda suke Zama barazana ga kasuwancin nasu, amma gwamnati ba ta yi wani abu ba domin ceto su.


 Sakataren ya yi nuni da cewa, bayan kokarin da aka yi na ci gaba da kasuwanci ba tare da kara farashin burodi ba, duk da karin farashin fulawa, Amma yanayin kasuwar ya tilastawa kungiyar ta dauki matakin, in ba haka ba mambobinta za su kasance cikin asara a koyaushe.


 Ya bayyana cewa kungiyar ta yi ta kokarin ganawa da shugabannin kamfanonin fulawa a kokarin da suke yi na rage farashin, amma kokarin nasu bai yi nasara ba saboda kamfanonin sun nuna cewa cutar COVID-19 a matsayin dalilin da ya sa taron ba zai kasance ba.


 Sakataren ya yi mamakin dalilin da ya sa farashin fulawar ya tashi daga Naira Dubu 9, 000 a karshen 2019 da farkon 2020 lokacin da canjin dala ya kasance N400 ko sama da haka, amma yanzu ya kai sama da Naira dubu16,000 yayin da farashin dala har yanzu bai fi N500 ba.
 Ya ce Fulawar IRS, wanda kamfanin BUA ya ke samarwa,wadda tayi ƙaranci a Kasuwa,ta fi kowacce tsada a kasuwannin.


 Yayi kira ga Abdussamad Isyaku Rabiu, Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA don rage farashin kayan fulawar sa, Sakataren ya kuma yi kira gare shi da ya Kara yawan samar da kayan sa domin a samu a kasuwa.


 Ya ce “Ina da kiraye-kiraye da yawa ga Abdussamad. Da farko dai, ya kamata ya inganta aikinsa domin samar da samfurinsa a kasuwanni.


 “Abu na biyu, ina kira ga Abdussamad da ya tabbatar an rage farashin fulawa. Maganar karin farashin fulawa na tafiya ne  kafada da kafada da canjin kudaden kasashen waje, Farashin fulawar da Naira Dubu 9, 000 a karshen 2019 da kuma farkon 2020 lokacin da canjin dala yake  ya kasance N400 ko sama da haka, amma yanzu ya kai Naira Dubu 16,000 yayin da har yanzu farashin dala bai fi N500 ba. Idan ka duba kari farashin ya kusan Mikawa.
 “Ina so in ja hankalin Abdussamad ya yi la’akari da halin da talakawa suke ciki sannan a rage farashin fulawar. Ya kuma kamata ya bamu dama mu masu yin burodin mu yi mu’amala kai tsaye da kamfaninsa.


 “Dalilin da yasa na faɗi haka, na kasance cikin wannan kasuwancin tsawon shekaru, amma ban taɓa samun tallafin Kamfanin ba ko ma da wakilin kamfanin BUA a gidan burodin na. Babu wakilin Kamfanin da ya zo ya wayar min da kai kan kayayyakin BUA su ba, “Sakataren ya koka
 Sakataren yace sun gudanar da babban taron Kungiyar su a ranar Laraba, kungiyar ta Kuma umarci mambobinta da su hadu da masu yin burodin na kasa-kasa a cikin kwanaki goma a wani yunkuri na fito da hanyoyin yin karin farashin ba zai haifar da damuwa ga jama’ar jihar Kano ba.


 Abdullahi ya roki gwamnati da ta duba masana’antun fulawa saboda, a cewarsa, Najeriya na fitar da alkama fiye da shinkafa, yana mai cewa idan aka waiwayi Masana’antun Matasa zasu Kara samun aikin yi sosai a bangaren fiye da abun da ake dashi yanzu haka.
 Ya gargadi gwamnati da kar ta bari kasuwancin ya durkushe saboda hanya ce ta samun kudin shiga ga dubban matasa a jihar Kano, yana mai cewa “a wannan kalubalen na tsaro, barin kasuwancinmu ya durkushe yana da hadari matuka.”


 A nasa bangaren, wani mai yin burodi, Abubakar Bello Ja’en, wanda shi ne manajan kamfanin ABJ Bread ya ce kasuwancin na fuskantar matsaloli da dama, galibi karin farashin fulawar ne Kuma ya haifar dasu.


 Ya bayyana cewa kungiyar ta sanar da su cewa ba za a shiga yajin aiki ba, amma dole ne su kara farashin burodin domin su ceci sana’ar su.


 Ya ce shawarar kara farashin ba zabin kungiyar ba ne, ya kara da cewa masu yin burodin suna son farashin fulawa ya ragu fiye da kara farashin burodin.


 “Bari in yi amfani da wannan damar in yi kira ga Abdussamad don yin la’akari da halin da mutane ke ciki na sauya farashin fulawar Kamfanin sa. Mutane na wahala, ba ma son karin kudin burodin, hakan ya saba wa burinmu,” in ji shi.

202 COMMENTS

  1. Бій Усика проти Джошуа відбудеться 25 вересня Про це офіційно оголошено 20 липня 2021 року. Для українського боксера Олександра Усика цей поєдинок… Усик – Джошуа: онлайн-трансляція чемпіонського бою Александр Усик – Энтони Джошуа – бой за титулы WBA, WBO, IBF, IBO в супертяжелом весе. Лоуренс Околи – Дилан Прасович – бой за титул WBO в первом тяжелом весе. Максим

  2. Роблес спрогнозировал исход поединка Усик – Джошуа – СПОРТ Александр Усик Энтони Джошуа смотреть онлайн Джошуа больше, богаче и авторитетнее Усика, но может проиграть. Сравниваем участников одного из главных поединков года. В субботу, 25 сентября, в Лондоне состоится поединок за звание

  3. Усик улетел на бой с Джошуа Украинец Александр Усик (18-0, 13 КО) улетел на поединок с чемпионом мира по версиям wbo, wba, ibf и ibo Энтони Джошуа (24-1, 22 КО). Об этом сообщил… Усик и Джошуа провели битву взглядов Последняя встреча Джошуа Усик смотреть онлайн Усик в костюмі Джокера вперше подивився в очі Джошуа (фото

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...

Shaye-shayen kwayoyi: Al’ummar Unguwar Rimin Kebe sun nemi agajin mahukunta

Daga Ibrahim Sani Gama   Kungiyar cigaban matasan unguwar Rimin Kebe...

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...