MAAUN ta taya Dalibanta Murnar cin Jarabawar ƙwarewa ta Jami’an Jinya da Ungozoma a Nigeria

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 
 Hukumar Gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha dake Niger (MAAUN), ta taya ɗalibanta daga Nijeriya waɗanda suka zauna jarabawar ƙwararru ta Hukumar dake kula da Jami’an jinya da Ungozoma ta Nigeria (NMCN), saboda nasarar da suka samu a jarabawar da Suka yi ta Shekarar 2021.


 Hukumar Kula da Malaman jinya da ungozoma a Najeriya ta fitar da sakamakon jarrabawar kwararru a ranar Laraba, 23 ga Yuni, 2021.


 Sakon taya murnar na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Shugaban Paris kuma Shugaban Jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya Sanyawa Hannu kuma aka aikowa Kadaura24.


 A cikin sanarwar, Farfesa Abubakar Gwarzo ya nuna farin cikin sa bisa nasarar da daliban suka samu, inda ya kara da cewa daliban sun sanya shi da jami’ar alfahari.


 “Shugaban Jami’ar ta MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo yayi matukar farin ciki da kwazon da daliban suka nuna , Sannan  yace  sun sanya jami’ar ta zama abar alfahari a duniya. Muna yi musu addu’ar samun nasara a duk abubuwan da suka sa a gaba kuma a duk inda suka samu kansu,” in ji  in ji sanarwar.


 Ya Kuma yi kira ga daliban da su ci gaba da yin aiki tukuru kuma a koyaushe su kasance jakadun makarantar na gari, Farfesa Abubakar Gwarzo ya kuma taya iyayen Daliban da su kansu daliban murnar Nasarar Jarabawar ta NMCN.

Farfesa Abubakar Adamu Gwarzo

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...