Dan Majalisar tarayya a Bichi Zai biyawa Dalibai 890 kudin Neco

Date:

Daga Mujibu Sani Dan zabuwa

Dan Majalisar Wakilai Mai Wakiltar Karamar Hukumar Bichi kuma Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan Ayyuka Hon Abubakar Kabir Abubakar ya amince da biyan kudin jarabawar NECO ga dalibai 890 da suka samu maki 6, 7, ko 8 a jarabawar ta Shekarar 2020/2021.


Wannan na kunshe ne Cikin Wata sanarwa da Dan Majalisar ya fitar a Sahihin shafinsa na Facebook .


 Sanarwar tace ana gayyatar ɗalibai zuwa FCE (T) Bichi a gobe Juma’a da ƙarfe 8 na safe tare Sannan kowanne Dalibi ana bukatar ya je da hotona 2 don rajista.  


An yi kira ga ɗaliban da su kasance tare da iyayensu ko masu kula da su zuwa wurin taron.
Kadaura24 ta rawaito cewa Ɗalibai da yawa sun Fadi jarrabawar qualifying wadda da ita gwamnatin jihar Kano take Amfani wajen tantance Waɗanda zata biyawa kudin jarrabawar kammala Sakandire ta Neco.


Sakamakon faduwa jarrabawar tasa al’umma da dama a Kano Musamman talakawa kokawa da yadda Sakamakon ya fita, Wanda hakan Wasu suke ganin gwamnatin tayi hakan ne da Gangan Saboda Kar ta biyawa Dalibai da yawa kudin jarrabawar.


Kun dai babban abun kokawar shi ne yadda aka saki Sakamakon jarrabawar a kurarren Lokaci Wanda shi Zai Hana Iyaye da yawa biyawa ‘ya’yansu kudin jarrabawar, Kuma Wasu Suna ganin Yara da yawa zasu iya Hakura da Karatun ma gaba Daya Saboda Rashin damar biyan kudin.

118 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba gaskiya a bayanin wasu Manoman Kano da suka ce Muna karbar kudi a wajensu – Civil defense

Rundunar tsaro ta Civil defense ta Kasa reshen jihar...

Korar ma’aikata a Kano: Bashir Gentile ya yiwa Faizu Alfindiki martani mai zafi

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Masanin kimiyar siyasa kuma mai sharhi...

Sakataren kungiyar NRO Abdulkadir Gude ya rasu

Allah ya yi wa dattijo, kuma Sakataren kungiyar Northern...

Gwamnatin da ta ke korar Ma’aikata ba ta Cancanci Wa’adi na biyu ba – Faizu Alfindiki

Daga  Maryam Muhammad Ibrahim   Abin takaici ne ganin yadda gwamnatin...