Annubar Kwalara :Sarkin Bichi ya jajantawa al’ummar sa

Date:

Daga Zahraddeen Sale

Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero ya mika Sakon ta’aziyyarsa da jaje ga wadanda suka kamu da cutar Amai da gudawa a karamar hukumar Bichi.


 Alhaji Nasir Ado Bayero ya ce yana cikin damuwa game da barkewar mummunar cutar.


 Mai Martaba Sarkin a cikin wata sanarwa da sakataren masarautar, Alhaji Abubakar Ibrahim Yakasai ya fitar ya bayyana cewa lokacin da lamarin ya faru Sarki baya gari Amma Daya samu labari ya yi gaggawar sanar da ma’aikatar lafiya ta jihar don Daukar Matakin Daya dace.


 Sarkin ya nuna damuwar sa tare da tabbatar da cewa masarautar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen neman samar da isassun kayan jin dadin jama’a ga yankin sa.


 Ya ce shi da kansa yana neman karin gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu da sauran kungiyoyi da nufin Kawo cigaba masarautar.


Mai Martaba Sarki Nasir Ado Bayero ya bukaci al’ummomin yankinsa da su Rika kula da kyawawan hanyoyin tsaftace muhalli.


 Ya kara da cewa yin riko da mafi kyawun tsabtar cutar zai taimaka masu sosai da kuma kiyaye su daga wasu cututtukan kasusuwa.


 Ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da ba wadanda suka kamu da cutar lafiya tare da jajantawa wadanda suka rasa ‘yan uwansu yayin annobar.


 Ya kuma yi addu’ar Allah ya kiyaye faruwar lamarin a nan gaba. 

131 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...