Hukumar Alhazai ta Kano zata fara Mayarwa Maniyata Kudinsu- Muhd Danbatta

Date:

Daga Halima M Abubakar

Hukumar Jin Dadin alhazai ta jihar Kano tace zata fara mayarwa Maniyata Aikin Hajjin bana kudaden su, Sakamakon Hana zuwa Aikin Hajjin da Kasar Saudiyya tayi Saboda Corona.

Sakataren Zartarwar Hukumar Alhaji Muhd Abba Danbatta ne ya bayyana hakan Yayin ganawarsa da Kadaura24 a ofishinsa.

Alhaji Muhd Abba Danbatta yace a Yau din Nan alhamis Hukumar zata Kara Kwamitin da Zai mayarwa Maniyatan kudaden da Suka Fara baiwa Hukumar.

Yace Kwamitin Zai Hadar da Masu Ruwa da tsaki a Hukumar da Kuma jami’ai daga Hukumomin Tsaro da Jami’i Daga Hukumar Hana cin hanci da rashawa domin Samun nasarar mayarwa Maniyata Kudinsu.

Yace kowanne lokaci Daga yanzu Maniyata zasu iya zuwa su karbi Kudinsu , sai dai yace za’a bada kudin ne ta banki da a Hannu ba.

Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a Ranar 11 ga watannan Hukumomi a Kasar Saudiyya Suka bayyana cewa baza su karbi Bakin Maniyata Aikin Hajjin bana ba Saboda Corona.

Shekaru biyu Kenan Corona tana Hana Aikin Hajjin a Dan Wannan taki.

322 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...