An tsinci Gawar Wani Jariri a Gezawa

Date:

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani jariri dan kwana daya da aka samu a cikin wata rijiya a Garin Tsalle da ke Karamar Hukumar Gezawa.


 Jami’in hulda da jama’a na hukumar Saminu Yusuf Abdullahi ya bayyana cewa, ana zargin cewa wasu da ba a san ko su wanene ba sun jefar da sabon jaririn a cikin rijiyar .


 Ya lura cewa hukumar kashe gobara ta jihar kano ta samu kiran gaggawa daga wani jami’in ta Abubakar Ibrahim Dandago, yana mai cewa Jami’an Rundunar na agaji ba su bata lokaci wajen dauke gawar jaririn da ya mutu daga rijiyar.


 Haka kuma, wani mutum mai suna Babawo Sulaiman dan shekara 35 ya rasa ransa a yayin wata gobara a wani wurin walda da ke titin Airport Road a Sabon Gari Kano.


 A cewar jami’in hulda da jama’a, mutum uku ne lamarin ya shafa wanda ya rasa ransa yayin da wasu ke karbar magani a asibitin kwararru na Murtala Muhammad.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...