Daga Abdullahi Kano
Wasu ‘yan daba sun kai hari ofishin’ yan Vigilantee dake unguwar Tunga ta karamar hukumar Kumbotso da ke jihar kano.
Da yake karin haske Dangane da lamarin ga manema labarai kwamandan kungiyar ‘yan Vigilanteen Tijjani muhammed Dattijo ya ce’ yan daban sun mamaye ofishin ‘yan bangar da misalin karfe 12:00 na Daren ranar Alhamis din data gabata dauke da muggan makamai, suka fasa ofishin suka lalata kayayyakin Ofishin da kayayyaki masu muhimmanci a ofishin.
“Yan daban basa Jin Dadin irin aiyukan da muke yi na Hana su gudanar da aiyukan ta’addanci a cikin wannan al’ummar, saboda mun dakatar da su daga aikata laifuka daban-daban a cikin wannan al’ummar”.
“Sun Kai Kimanin su sittin da Suka zo suka Yi mana barna a ofishin mu , Sannan kuma sun yi amfani da wuka Mai kaifi wajen gutsirewa Wani yaro Almajiri dan yatsansa yaron da Bai ji ba Bai gani ba, yanzu Haka dai yana karbar magani a asibitin Murtala Mohammad” Inji kwamandan
Kwamanda Tijjani Muhammed Dattijo ya ce bayan ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda an cafke mutum takwas da ake zargi.
Ya yi kira ga iyaye da ke zaune a unguwar Tunga da su yi taka-tsan-tsan da sanin inda yaran suke, musamman abokan da suke yawo tare da su, yana mai cewa kungiyar ’yan banga za ta yi jinkirin tabbatar da tsaro a Yankin.
Ya yaba da goyon baya da hadin kai da Ofishin rundunar ‘yan sandan reshen Dorayi babba take ba su.
“DPO yana kan aiki koyaushe don tabbatar da cewa an dakile dukkan ayyukan sata a cikin wannan al’umma, jami’i ne mai matukar kokari, muna yabawa kokarinsa”.
Lokacin da Wakilin Majiyar Kadaura24 ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na ’yan sanda na rundunar ta Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Wasu ‘yan daba sun kai hari ofishin’ yan banga da ke tunga, kuma suka lalata duk wani abu mai muhimmanci a ofishin ‘yan sintirin, mun cafke takwas daga cikin wadanda ake zargin, kuma za a mika su zuwa CID don ci gaba da bincike.”
“Muna tabbatar wa jama’ar Tunga da sauran jama’a cewa maharan ba su da wurin buya a Kano, za mu Kamo su kuma idan an same su da laifi za a hukunta su
Allah yai mana tsari da mugun mutane
A gaskiya yan Vigilante suna matukar kokari wajen samar da tsaro a unguwanninmu