Tsaftar Muhalli: Gwamnatin Kano tayi Sammaci Shugabannin Kasuwar Rimi

Date:

Daga Sani Magaji Garko

Gwamnatin jihar Kano ta yi sammacin shugabannin kasuwar Rimi sakamakon kazartar kasuwar da kuma cushewar magudanan ruwan ta.

Kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan bayan kammala tsaftar Muhalli da ake gudanarwa a duk Asabar din karshen wata.

Kwamishinan ya bayyana takaicinsa sakamakon halin ko in kula da shugabannin kasuwar suka nuna duk da wata kungiya Mai suna “Mama Initiative” ta na share kasuwar Amma Babu Koda wakili daga kasuwar inda ya ce Gwamnati ba zata lamunci hakan ba.

Dakta Kabiru Getso ya ce a shekarar da ta gabata Gwamnatin jihar Kano ta kashe miliyoyin nairori musamman dan yashe Magudanan ruwa ciki harda na kasuwar amma halin ko in kula da shugabannin kasuwar suka nuna yasa yanzu Magudanan ruwa kasuwar duk sun kusa cikewa.

Kwamishinan ya kuma yabawa jami’an tsaro musamman Yan sanda da ‘yan kungiyar Vijilantee bisa yadda suka bada gudun mowa domin tabbatar da doka inda ya ce maaikatar Muhalli zata rubuta takardar yabo ga kwamishinan Yan sanda bisa irin kokarin da jami’an sa suka yi na tabbatar da doka.

Dakta Kabiru Getso ya kuma bukaci shugabannin tashoshin motar Kano Line da NARTO dake Kofar Nasarawa da su tabbatar sun hada kan maaikatan su tare da share tashar kasancewar an same su cikin datti a lokacin tsaftar Muhallin.

Kadaura24 ta rawaito Kwamishinan Muhallin ya yabawa al’ummar jihar Kano bisa irin hadin kan da suke bayarwa inda ya bukace su dasu hada hanu da kungiyoyi masu zaman kansu domin tsaftace loko da sako na jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zaizayar kasa: Gwamna Abba gida-gida ya raba diyyar Naira Miliyan 600 A Kano

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Dalilin da ya hana Sarki Aminu Ado Bayero zuwa gidan yari na goron dutse a yau alhamis

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Rahotanni sun tabbatar da cewa Sarkin...

Matakai 3 da gwamnatin Kano ta dauka kan kafafen yada labarai a jihar

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnatin jihar Kano ta ce a...

Yadda manoma a Kano suka zargi jami’an Civil defense da karbar kudade a wajensu

Daga Umar Ibrahim kyarana   Manoman dajin dansoshiya dake karamar hukumar...