El-Rufa’i ya Kori Mutane 19 Daga Gwamnatinsa

Date:

Daga Safyan Dantala Jobawa

Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya amince da korar masu taimaka masa na musamman guda 19 daga aiki.

A cewar wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a yau Laraba, wannan ne zagayen farko na masu muƙamana siyasa da za a kora a yunƙurin da gwamnan ke yi na rage yawan ma’aikatan gwamnati.

Daga cikin waɗanda aka kora akwai mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati da babban darakta a hukumar Public Procurement Authority.

Gwamna El-Rufai ya sha suka game da korar ma’aikata kusan 7,000 da ya yi, abin da ya jawo yajin aikin ma’aikata na kwana huɗu a jihar.

Sai dai gwamnatin na kare matakin da cewa tana kashe kusan kashi 80 cikin 100 na kuɗin da take samu wajen biyan albashi.

95 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya bijiro da harajin da zai sa farashin man fetur ya karu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar...

Sabbin Nau’o’in cutar Shan Inna 4 sun bulla a Kano

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar...

NDLEA ‘Yan Sanda da Gwamnatin Kebbi Sun Karyata Jita-jitar Samar da Filin Jirgin Sama na Boye a jihar

  Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta...

Kotu a Kano ta kawo karshen Shari’ar wata Tunkiya

Daga Dantala Uba Nuhu, Kura An kawo ƙarshen shari’ar wata...