Taimakon Junanmu yasa Muka sake Haduwa – PDMC 2015

Date:

Rabi’u Usman

Kungiyar tsoffin Daliban Makarantar Kwalejin Aminu Kano, Wadda akafi Sani da Aminu Kano College of Islamic and legal studies (Legal) Sashen Koyon aikin Jarida (Professional Diploma in Mass Communication PDMC) na Shekarar 2015 sun Bayar da Tallafin Kayan Abinci da Kudin Cefane ga iyalan Mutane Biyu daga Cikin yan Uwan Su Dalibai wanda Suka Rasu.

Hakan ta faru ne Daidai Lokacin da Tsoffin Daliban Suka Samar da Cikakken Hadin Kai a tsakaninsu Domin Warware Wasu Matsaloli da Ka iya Fuskantar su a kowanne lokaci, Wanda Suke Taimakawa Junan Su ta Fannoni Daban Daban Kamar yanda Shugaban Kungiyar Daliban Jamilu Dan Mudi ke Shaidawa Wakilin Kadaura24 Rabi’u Usman.

Yana Mai Cewar an Samar da Wannan Gidauniyar ne Don Taimakon Kai da Kai a kowanne lokaci Don Warware Matsalolin da Ka iya kunno Kai da Ba’a San Zuwan ta ba.

A Nasu Bangaren Iyalan Rabi’u Haruna Al – Rahuz da Kuma Dahiru Musa Sun Bayyana Jin Dadin Su da Wannan Kungiyar tsoffin Daliban da Suka Taimaka Musu da Kayan Abinci da Kuma Kudin Cefane na ganin Har yanzu Ba’a Manta da Su ba duk da cewa, yanzu Haka Mamatan sunkai Kimanin Shekaru Sama da 4 da Rasuwa, har yanzu ana Cigaba da Taimaka Musu ta Kowacce fuska.

A Karshe dai Kakakin Kungiyar Mukhtar Ali Tukura yayi Addu’ar Samun Ragamar Ubangiji Madaukakin Sarki ga Wadannan Mamatan da Suka Rasu, da Kuma Fatan Allah yasa Muyi Kyakkyawan Karshe.

16 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...