Daga Nasiru Sani Diso
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari na cikin gida da na waje, FDI, don bunkasa tattalin arzikin jihar nan.
Gwamnan ya yi wannan ikirarin ne a karshen mako, lokacin da ya kaddamar da Wani kamfanin Da aka Kashe magudan biliyoyin Nairori daya ke guda Cikin mallakin kamfanin Lee Group , a Tokarawa, da ke wajen babban birnin jihar.
Cikin Wata sanarwa da Babban Darktan Kafafen yada labarai da Hulda da jama’a na Gidan Gwamnati Ameen K Yassar ya aikowa Kadaura24 yace Wannan na zuwa jim kadan da gwamnatin jihar ta bayar da fili ga rukunin kamfanonin Lee, a Bagadawa, karamar hukumar Dawakin Tofa, don ba su damar kafa filin shakatawa na masana’antu, wanda ke da nufin juya akalar tattalin arzikin jihar.
“A matsayin Kano na daya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a Najeriya kuma mafi yawan mutane a kasar nan, mu a matsayinmu na gwamnati, ya zama wajibi mu tabbatar da saukin kasuwanci ta yadda za mu iya ciyar da jihar zuwa cibiyar kasuwancin da masana’antu a kasar gaba” Inji Ganduje
“Lokacin da aka kafa masana’antu da yawa, tattalin arziƙi yana ci gaba da haɓaka, gwamnati na samun kuɗaɗen shiga don magance matsalolin kuma yawancin matasanmu suna samun ayyukan yi”. Ganduje
Don haka Gwamna Ganduje ya bayyana kafa kamfanin Top Pan Nigeria Ltd. a Kano, a matsayin abin da Zai bunkasa tattalin arziki, tunda kamfanoni a jihar nan yake ba za su sake fita waje ba don sayen Kayan aikinsu.
A nasa jawabinsa Mukaddashin Shugaban rukunin kamfanonin Lee Group, Ahmadu Haruna Zago, ya bayyana cewa dukkanin kayan da suke da su an same su ne daga Legas kuma kusan dukkanin ma’aikatanmu matasa ne daga Kano. Manufarmu ita ce samar da ayyukan yi, ta hanyar kamfanoninmu, na akalla mutane dubu 50″.
Alhaji Ahmadu, wanda ya godewa gwamnati saboda karfafa gwiwar Lee Group, ta hanyar aiwatar da abubuwa da yawa, amma duk da haka ya bukaci gwamnatin Ganduje da ta kara himma wajen magance kalubalen samar da ruwan sha da ke fuskantar wasu kamfanonin nasu.