Duk maniyacin da ba a yiwa Rigakafin corona ba, ba zai je aikin hajjin bana ba-Muhd Abba

Date:

Munirat Ahmad Sagagi

Hukumar Jin Dadin alhazai ta jihar Kano ta Kammala Gina Asibiti a Sansanin alhazai, Inda ta Kashe Sama da Naira Miliyan 44 wajen Gina Asibitin da Sanya Kayan Aiki acikinsa.


Shugaban Hukumar Jin Dadin alhazai ta jihar Kano Alhaji Muhd Abba Danbatta ne ya bayyana hakan Yayin da yake yiwa Manema labarai Karin Gaske game da shirye-shiryen Aikin Hajjin bana.
Alh. Muhd Abba yace Gwamna Dr Abdullah Umar Ganduje ya damu matuka da al’amarin da ya shafi Jin dadin Maniyata tun Daga gida Nigeria har zuwa Kasa Mai tsarki.


Yace an Samar da Asibitin ne domin gudanar da kwaje-kwajen da ake Bukata ga Maniyata tare Kuma da kula da lafiyar Maniyatan yayin da suke zaman Sansanin alhazai Kafin tashinsu zuwa Kasa Mai tsarki. 



Danbatta yace bayan Kammala bitar alhazai ta sati-sati da akai, yanzu za’a fara gudanar da bita ta kullum-Kullum a Dukkanin cibiyoyin bita dake fadin jihar Kano.


Alhaji Muhd Abba Danbatta ya Kara da cewa yanzu haka Jami’an lafiya dake Hukumar zasu fara yiwa maniyata allurar rigakafin Corona zagaye na 2 a ranar Talata 24 ga Watan Mayun Shekara ta 2021.



Shugaban Hukumar Jin Dadin alhazan yace Duk Wanda Bai Yi allurar rigakafin Corona kashi na farko ba , bazai samu Damar zuwa Kasa Mai tsarki ba a Wannan Shekara Saboda da kuracewar lokaci.


Ya bukaci maniyata Aikin Hajjin bana dasu dage da zuwa wajen bita domin su gudanar da Ibadar su Cikin ilimi kamar yadda yake a addinin Musulunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...