Hawan Nasarawa: Iya Mu’amalarka tasa kowa yake Murnar Zaman ka Sarkin Kano – Ganduje

Date:

Daga Surayya Abdullah Tukuntawa

Gwamna jihar Kano Dr Abdullah Umar Ganduje yace Iya Mu’amalarka tasa Kowa a jihar Kano da Kasa baki Daya yake Murna da ka Zama Sarkin Kano.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne Yayin Hawan Nasarawa Wanda Sarkin Kano yake kaiwa Gwamnan Kano Ziyarar Barka da Sallah har zuwa gidan Gwamnati.

Gwamna Ganduje yace Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya fada Masa cewa Yana Murna da Nadin Sakin a Matsayin Sarkin Kano Saboda yadda Sarkin take kaunar Zaman lafiya da kowa.

” Sarakunan Nigeria da yawansu sun fadamin cewa sun ji Dadin Ziyarar sada zumunci da kakai musu, kuma a Kano kana zaune da Malamai Lafiya, kana zaune da Attajirai Lafiya Kuma Kana zaune da duk al’ummar jihar Kano lafiya to Haka ake Son Shugaba ya Zama”. Inji Ganduje

Gwamnan yace idan yaga Alhaji Aminu Ado Bayero Yana tuna Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Dr Ado Bayero Saboda sun yi kamanceceniya a kamanni da Kuma halaye da Dabi’unsu.

Yace Muna Jin Dadin shawarwarin da Sarkin Kano yake baiwa gwamnati da Kuma yadda yake Girmamamu Kuma muma make girmamama shi Saboda baya yin abubun da basu dace ba.

” Mai Martaba Sarki kalamanka akwai girmamawa a Cikin su, Kuma Dama ana auna kowacce al’umma ne da irin kalaman Shugabanin ta, Babu shakka Muna alfahari dakai a Matsayin Sarkinmu Mai Albarka”.

1 COMMENT

  1. Hausawa suna cewa Maso uwa ya so Danta, Ni Masoyi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ne nahakika haka kuma Allah ya Jarrabeni da Son Sabon Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Ni Mutumin Azare ne Katagum Bauchi State Kuma Munji dadi Ziyarar da Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya Kowa Azare daga Abubakar Sani Chinade

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya bijiro da harajin da zai sa farashin man fetur ya karu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar...

Sabbin Nau’o’in cutar Shan Inna 4 sun bulla a Kano

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar...

NDLEA ‘Yan Sanda da Gwamnatin Kebbi Sun Karyata Jita-jitar Samar da Filin Jirgin Sama na Boye a jihar

  Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta...

Kotu a Kano ta kawo karshen Shari’ar wata Tunkiya

Daga Dantala Uba Nuhu, Kura An kawo ƙarshen shari’ar wata...