Daga Kamal Yusuf Daneji
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci Fulani makiyaya Yan asalin jihar Kano wadanda suke gudanar da harkokin su na kiwo a kudancin Kasar nan dasu dawo Kano domin kaucewa tsangwamar da ake yi musu a Wasu shiyoyin Nigeria.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne Yayin daya karbi bakuncin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a Gidan Gwamnati Wanda zaje domin Taya Gwamnan Murnar Sallah Karama yayin Hawan Nasarawa.
Gwamnan yace ana tsangwamar Fulani a wasu shiyoyin Nigeria kawai Saboda suna yawon kiwata Dabbobin su, inda yace kamata yayi fulanin su hakura da tsohon tsarin kiwo irin na da Wanda shi ne yake jawowa fulanin Tsangwama a Cikin al’umma.
Yace gwamnatin jihar Kano tayi tanadi na musamman domin magance tsohon tsarin kiwon, Inda yace gwamnati ta Samar da wajen kiwo na zamani a dajin Dan soshiya domin magance Matsalolin tsaro da Kuma Kara inganta sha’anin kiwo.
Ganduje ya kalubalanci Wasu Daga Cikin fulanin wadanda suke harkokin Ta’addanci Wanda yace hakan ba dai-dai ba ne, yace kamata yayi su nemi Ilimin addini Dana zamani domin gujewa shiga harkokin da basu dace ba Cikin jahilci.
Ya yabawa Sarkin na Kano da ya Kai masa Wannan ziyara ta sada zumunci wadda ya gada Daga magabatansa ,yace Yana matukar Jin Dadin shawarwarin da Sarkin yake baiwa gwamnatin wadanda suke taimakawa wajen Kara bijiro da aiyukan da zasu ciyar da Jihar nan gaba.
Kadaura24 ta rawaito Ganduje ya baiyanawa Sarkin na Kano irin aiyukan da gwamnatinsa take yi a fannin ilimi, Lafiya, Kasuwanci, da aiyukan Raya Kasa wadanda yace Suna Kara Daga darajar jihar Kano a idanun Duniya.
Ya Kuma yabawa Mai Martaba Sarkin bisa irin Gudunmawar da suke bayarwa wajen inganta harkokin Tsaro a Kano Baki Daya, tare Kuma da ba shi tabbacin gwamnatin jihar Kano Zata cigaba da bijiro da sabbin Tsare-tsare Domin cigaban jihar Kano.
A nasa Jawabin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya Gwamnan Murnar Sallah Karama tare Kuma da yadda gwamnatin take gudanar da aiyukan da suke ciyar da Kano gaba.
Sarkin yace a Matsayinsa na Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kano Zasu cigaba da baiwa gwamnatin Kano hadin Kai da goyon bayan domin taci gaba da hidimtawa al’ummar jihar Nan.