Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sakon gaisuwarsa ga Musulman kasar da ma na kasashen waje a yayin da ake shirin yin sallar Idi.
Wata sanarwa da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar ya aike wa manema labarai ranar Laraba ta ambato Shugaba Buhari yana fatan za a gudanar da bukukuwan sallah cikin “zaman lafiya, tsaro da ‘yan uwatantaka da kuma kauna ga kowa.”
Ya kara da cewa hadin kai tsakanin Musulmai da Kiristoci yana da matukar muhimmanci musamman a wannan lokaci da kasar take fama da kalubale daban-daban.
“Ya kamata mu yi addu’a tare a kan matsalolin garkuwa da mutane da hare-haren ‘yan bindiga da kuma masu neman mulkin siyasa ta hanyar shafa kashin-kaji domin ganin kasarmu ba ta ci gaba da kasance a dunkule ba,” in ji Buhari.
Shugaban kasar ya hori shugabannin siyasa da na addini da kuma masu rike da sarautun gargajiya su karfafa gwiwar ‘yan kasar wajen ganin sun kaunaci juna da kuma tausawa juna.