Sallah: Hukumar Karota zata tura Jami’an ta 1000, tare da Hukunta Masu tukin Ganganci yayi bikin Sallah

Date:

Daga Halima A Musa

A kokarin ta na tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa a cikin jihar Kano ba tare da Wata matsala ba Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano (KAROTA) tace ta kammala shirye-shiryen tura akalla ma’aikata 1000 fadin jihar nan a yayin bukukuwan Sallah mai zuwa tare da sauran hukumomin tsaro. 

 
 Hukumar ta ga dacewar tura dimbin ma’aikatanta a lokacin bikin duba da yawan fitowar motoci da sauran masu amfani da hanyar da ake yi a  lokaci irin Wannan.


 Hukumar ta Karota ta Bukaci jami’an da su tabbatar da masu ababen hawa da sauran masu amfani da tituna suna bin duk dokokin tuki na jihar Kano don ganin ba a Sami cunkosun ababen hawa a jihar nan ba kamar yadda aka saba.


 Cikin Wata sanarwa da Jami’in Hulda da jama’a na Hukumar Nabulisi Abubakar K/ Na’isa ya aikowa Kadaura24 yace KAROTA ta yi gargadin cewa Hukumar za ta kama tare da hukunta duk wanda ya karya dokar hanya a yayin bukukuwan Sallah saboda wasu marasa kishi suna mayar da lokacin na yin ganganci da ababen hawa Wanda Kuma hakan na jefa rayukansu da na Wasu Cikin hadari.


 Manajan Darakta, Hon. Baffa Babba Dan’agundi ya gargadi iyaye da su guji dabi’ar ba yaransu abin hawa don tuki musamman a wannan lokacin domin duk wani yaro da aka anshi yana tuki za a kama shi, a ci shi tararsa da Kuma kwace masa abin hawa.


 Sauran laifukan zirga-zirgar sun hada da;  rashin bin ka’idojin tuki Wanda aka tanadi hukuncin a karkashin sashi na 16 (4,7 & 8) Sakin layi na 12 na dokar KAROTA 2012 wacce ta bada damar cin tarar N15,000.


 Bugu da ƙari kuma, Tuka baburan Masu kafa Uku ( Adaidata sahu) ga Yara Masu ƙarancin shekaru za’a ci tararsu N20,000, hukunci a ƙarƙashin sashi na 16 sub, 4,7 & 8 Sakin layi na 2, 3 na dokar KAROTA Law 2012.


 Don haka ana shawartar jama’a da duk masu amfani da hanya da su bi dukkan dokokin hanya kafin, lokacin da bayan bukukuwan Sallah don kaucewa abin takaici da ka iya haifar da rauni, asarar rayuka ko dukiyoyi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...