Wani Magidanci anan Kano ya koka bisa yadda ake neman cin zarafinsa akan Cikon kudin Hayar gidan da yake ciki shi da Iyalansa.
Magidanci Mai Suna Muhd Lawan Wanda ya zanta da Jaridar Kadaura24 Cikin halin damuwa yace Mai gidan da yake haya a gidansa yasha alwashin sawa ayi wasi da kayansa matukar ya Gaza Cika Masa kudin hayar gidansa.
“Naira Dubu 50 nake biya Duk Shekara to Wannan Shekarar Cikin ikon Allah Naira Dubu 25 kawi na iya biya Saboda halin Rayuwa, gashi wa’adin da aka dibar min ya zo Karshe har na Nemi Kari kuma shi ma karin Yanzu Haka ya zo Karshe Amma bani da abun da Zan bayar”Inji Magidancin
Yace a Wannan Azumi kusan Dan abun da nake samu a abun da zamuci ni da iyali yake tafiya, Kuma ga yawan sallamar Masu gida da kulum ake Yi min na na biya Cikon kudin.
Malam Muhd yace ban so nayi roko ba , Amma bani da wata hanya data fi yin hakan ,dalilin Kenan da yasa nake neman tallafin Yan uwana Musulmi da kada su Bari na tozarta ni da iyali na.
Ga Wanda yake son tallafawa Wannan bawan Allah ya ya kirawo mu a Wannan Lambar 0813 741 2709.
Hakika Manzon Allah (S A W) yace Allah yana tausayawa Wanda yake tausayawa Bayinsa, Allah ya bada ikon taimakawa Ameen.