Gwamnatin Kano da Hadin Gwiwar Asibitin Idon na Makka zasu yiwa Mutane Dubu 6 Aikin Ido kyauta.

Date:

 Daga Abdulrashid B Imam


 Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar Asibitin kwararrun Ido na Makka sun fara aikin duba ido kyauta a cibiyoyin kula da lafiyar ido a Matakin guda 12 da aka kafa kwanan nan a kananan hukumomi goma sha biyu da aka zaba a jihar nan.


 Da yake karin haske kan aikin, Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Dokta Tijjani Hussain ya bayyana cewa, shirin na daga cikin yarjejeniyar da aka sanya wa hannu tsakanin Asibitin Idon na makka da kuma Gwamnatin Jihar Kano da nufin gudanar da aikin duba lafiyar ido kyauta a duk shekara ga al’umma a cibiyoyin kula da lafiya matakin farko goma sha biyu da aka zaba domin kula da ido na farko.


Cikin sanarwar da Jami’in Hulda da jama’a na Hukumar Maikudi Muhammad Marafa ya ail Kadaura24 yace Dakta Hussain ya ci gaba da cewa, shirin wanda aka fara shi a karamar hukumar Tsanyawa za’a yi shi tsawon kwanaki 4, inda ake sa ran sama da mutane 6,000 da aka zabo daga kananan hukumomi 12 da aka zaba za su amfana da aikin duba idanun kyauta.


 A nasa jawabin, Babban Jami’in kula da lafiyar ido a Hukumar kula da lafiya a Matakin farko ta jihar kano Malam Kamilu Saleh ya bayyana cewa, aikin ya kunshi duba mutane tare da samar da magunguna ga marasa lafiyar Ido kyauta.


 Ya bayyana cewa, Fiye da mutane 6,000 da aka zabo daga Hukumar Kula da Kiwon Lafiya a matakin farko 12 ake sa ran za su ci gajiyar aikin, yayin da 180 za su ci gajiyar tiyatar Ido , yana mai jaddada cewa mutane 110 za su za’a yi musu aikin  ido na kyauta daga karamar Hukumar Tsanyawa.   

    A nasa jawabin, Hakimin karamar hukumar Tsanyawa Alhaji Dayyabu Aliyu Fama ya yaba wa kokarin wannan gwamnati kan kokarin da take yi na gudanar da aikin duba lafiyar idanun kyauta kuma ya yi kira ga jama’ar jihar Kano da su ba Gwamnatin Kano hadin kai a kokarinta na inganta lafiyar mutanen jihar Nan .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...