Kowanne lokaci daga yanzu Yan kwangilar Hanyar Gwarzo zuwa Dayi zasu dawo aiki – Sanata Barau Jibril

Date:

Daga Abubakar Sadeeq

Sanatan Kano ta Arewa Sanata Barau I Jibril yace kowanne lokaci daga yanzu Yan kwangilar da suke aikin hanyar data tashi daga Kabuga zuwa Gwarzo ta wuce Garin Dayi dake jihar Katsina zasu dawo bakin aikinsu.

Sanata Barau Jibril ya bayyana hakan ne Yayin da yake Zantawa da Jaridar Kadaura24 a yammacin Talatar nan ta wayar tarho.

Sanata Barau Jibril dai Dama shi ne ya Kawo aikin hanyar wadda ta Dade tana ciwa al’ummar yankin tuwo a kwarya Saboda lalacewar da hanyar ta yi.

Sanatan yace Yan kwangilar sun gana da Daraktan aiyuka na Ma’aikatar aiyuka da gidaje ta gwamnatin Tarayya a Abuja inda Suka Tattauna muhimman batutuwan yadda za’a dawo a cigaba da aikin domin saukakawa al’ummar yankin.

“Daga Wannan cigaba da aka samu Yan kwangilar sun tabbatarmin kowanne lokaci daga yanzu zasu dawo bakin aikinsu domin kammala Wannan gagarumin aikin hanyar wadda al’ummar Suka Dade suna bukata”. inji Sanata Barau Jibril

Yace kammala aikin hanyar data tashi daga Kabuga zuwa Rimin Gado zuwa Garo zuwa Gwarzo ta wuce har zuwa Dayi Zai taimaka tattalin arzikin yankin da Kuma baiwa Manoma damar fito da amfanin gonarsu Cikin Sauki.

Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa Sanata Barau Jibril ne ya gabatar da kudirin gyaran Hanyar a zauren Majalisar Dattijai Kuma gwamnatin Tarayya karkashin shugaba Muhd Buhari ta fitar da makudan kudade domin aiwatar da aikin don amfanin al’ummar jihohin Kano da Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba gaskiya a bayanin wasu Manoman Kano da suka ce Muna karbar kudi a wajensu – Civil defense

Rundunar tsaro ta Civil defense ta Kasa reshen jihar...

Korar ma’aikata a Kano: Bashir Gentile ya yiwa Faizu Alfindiki martani mai zafi

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Masanin kimiyar siyasa kuma mai sharhi...

Sakataren kungiyar NRO Abdulkadir Gude ya rasu

Allah ya yi wa dattijo, kuma Sakataren kungiyar Northern...

Gwamnatin da ta ke korar Ma’aikata ba ta Cancanci Wa’adi na biyu ba – Faizu Alfindiki

Daga  Maryam Muhammad Ibrahim   Abin takaici ne ganin yadda gwamnatin...