Daga Jamila Sulaiman Aliyu
Hukumar Hisba ta jihar Kano ta Kori daya daga cikin manyan jami’anta, Sani Nasidi Uba, wanda aka fi sani da Sani Remo saboda haifar da abin kunya ga rundunar.”
Kwamitin da Kwamandan Janar, Ustaz Harun Muhammad Ibn Sina ya kafa, ya tuhumi Sani Rimo da samunsa da wani mummunan laifi.
Sani Rimo wanda aka san shi a sahun gaba wajen kamen karuwai da sauran ‘yan mata marasa gaskiya, an kama shi ne a cikin watan Faburairun bana tare da wata matar aure a wani dakin otal da ke yankin Sabon Gari a babban birnin jihar Kano.
Jami’in ya fadawa rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano cewa matar da ake magana a kai‘ yar dan uwansa ce wacce suke samun matsala da mijinta.
A cewarsa, ya ajiye ta a dakin otel har zuwa lokacin da za a warware matsalolin.