Daga Safiya Ibrahim Gwagwarwa
Manajan Darakta kuma Babban Darakta, Dakta Jamil Isyaku Gwamna a madadin Manajan da Hukumar Gudanarwar Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya jinjina wa gudummawar da ‘yan jarida ke bayarwa ga ci gaban kasa.
A cewar Dakta Gwamna, KEDCO ba a bar ta ba a tasirin kafafen yada labarai kasancewar sun kasance ababen dogaro a tafiyar da KEDCO ke Yi a yanzu.
Cikin Wata sanarwa da shugaban sashin yada labarai na kamfanin Kedco Ibrahim Sani Shawai ya aikowa Kadaura24 yace
Wannan shine dalilin da ya sa muke kuma yin amfani da lokacin don jinjina wa maza da matan Yan jaridu dangane da wannan babbar ranar.
Dangane da wannan, KEDCO tana yiwa dukkan kayan aikin jarida murnar Ranar ‘Yancin’ Yan Jarida ta Duniya tare da fatan kungiyoyin ‘yan jaridu za su ci gaba da hadaka da KEDCO don inganta tsarin isar da sakonni ga dimbin kwastomomin da ke fadin Jihohin Kano, Katsina da Jigawa.