An harbe wani babban malami yana jan sallar Asham

Date:

An harbe wani babban malami yana jan sallar Asham

An harbe wani babban malamin addinin Musulunci a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

An yi wa Sheikh Ali Amini, ruwan albarussai yayin da yake jagorantar sallar Asham a ranar Asabar a cikin babban masallacin garin Beni.

Har yanzu dai ba a bayyana waɗanda suka aikata kisan ba.

Tun da farko wasu da ake zargin ‘yan tawayen ADF ne sun kai hari kan wasu ƙauyuka biyu a yankin.

Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce an kashe mutane 19 ciki har da sojoji da dama.

Yayin da ƴan ƙasar ke ƙara fusata kan yawaitar hare-haren ƴan tawaye, shugaban kasar Felix Tshisekedi a ranar Juma’a ya ayyana wani mataki na yi wa lardunan Arewacin Kivu da Ituri ƙawanya- matakin da ake ganin zai bai wa sojojin Congo karin karfi da ƙwarin gwiwa

57 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...